Babachir ya karɓi na goro daga hannun yan kwangila

Babachir ya karɓi na goro daga hannun yan kwangila

-Rahoton kwamitin bincike na majalisar dattawa ya kama Babachir da hannu dumu dumu cikin cin hanci da rashawa

-Shugaban kwamitin Shehu Sani ya bukaci a gurfanar da Babachir gaban kuliyan manta sabo

Rahoton kwamitin majalisar dattawa ya bankado wasu makudan kudade da suke zargin dakataccen sakataren gwamnati Babachir David Lawal ya amsa daga hannun yan kwangila.

Kwamitin tace yan kwangilan sun biya kudaden ne ga kamfanin Rholavision, mallakin Babachir, kuma ana sa ran zata mika rahoton tag a majalisar a zaman ta na yau.

KU KARANTA: “Awanni 2 muka kwashe da Buhari muna tattaunawa” – shugaban NNPC

Jaridar Daily Trust tayi arba da rahoton kwamitin, wanda yace yan kwangila guda bakwai ne suka biya kamfanin Babachir naira miliyan 507 cikin asusun ajiyan bankin kamfanin.

Rahoton yace, wani kamfani mai suna JOSMON technologies daya samu kwangila har guda biyu na kusan miliyan 530 ya sanya naira miliyan 317 cikin asusun kamfanin Babachir David Lawal ta hanyar aikawa da kudaden ha sau 23.

Babachir ya karɓi na goro daga hannun yan kwangila

Babachir

Haka zalika, wata kamfani mai suna JMI Global technologies ta samu kwangila guda 8 daya kai na naira kiliyan 199, amma sai ta sanya naira miliyan 30 cikin asusun bankin Rholavision kamfanin Babachir dake Bankin Ecobank daga wani asusun Zenith Bank mai lamba 114357188.

Sai wani kamfani mai suna Messers Adamawa Borehole and Drilling Company daya samu kwangilar gyaran azuzuwa 18 a makarantar sakandari ta yan mata dake Yeskule a garin Michika da aka biya naira miliyan 54.8, shima kamfanin ya sanya ma Babachir naira miliyan 18.3 a asusun bankin.

Kamfanin Yuby Ventures Limited sun samu kwangilar gina azuzuwa 15 a makarantar Firamari na Hausari a Adamawa ta biya kamfanin Babachir naira miliyan 58. Shima wani kamfani mai suna Barde Brothers multi-service limited da suka samu kwangilar gyaran azuzuwa, kuma aka biya su naira miliyan 145.6 sun biya kamfanin Rholavision na Babachir naira miliyan 84.

Shugaban kwamitin, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar “A yayin binciken mu, mun gano Rholavision ta karbi cin hanci daga hannun yan kwangila ta asusun bankin kamfanin dake Ecobank mai lamba 0182001809.

“Sa’annan babban bankin Najeriya, CBN, ta tabbatar mana cewar har yanzu Babachir ne kadai ke da daman cire kudi a wannan asusun bankin, da sauran asusu 13 na kamfanin Rholavision, kwamitin ta tabbatar cewa Babachir yayi karya dokar aikin gwamnati tare da cin mutuncin rantsuwar kama aiki, don haka a gurfanar da shi gaban kotu.”

Daga karshe kwamitin ya bada shawarar hukumomi dake da hakkin kula da bada kwangila su tabbatar an kammala ayyukan da aka bayar tare da biyan kudaden cikakku.

NAIJ.com ta ruwaito a yau ake sa ran kwamitin Osinbajo zata mika ma shugaba Buhari sakamkon binciken data gudanar akan Babachir.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan Najeriya yace yayi dana sanin zaban APC

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel