“Awanni 2 muka kwashe da Buhari muna tattaunawa” – shugaban NNPC

“Awanni 2 muka kwashe da Buhari muna tattaunawa” – shugaban NNPC

-A jiya ne shugaba Buhari ya dawo bakin aiki, inda ya karbi bakoncin shugaban NNPC

-Shugaban NNPC, Maikanti Baru ya kwashe awanni 2 da shugaba Buhari

Shugaban rukunin kamfanin matatan man fetur na Najeriya, NNPC, Maikanti Baru yayi gemu da gemu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata 2 ga watan Mayu, inda ya bashi rahoton batutuwan da suka shafi harkar man fetur a Najeriya.

Maikanti Baru ya bayyana haka ne yayin dayake ganawa da manema labaru dake fadar shugaban kasa bayan ya gana da shugaba Buhari, inda yace shugaba Buhari ya nuna farin cikinsa bisa daidaito da aka samu a bangaren hada hadan man fetur.

KU KARANTA: Rikicin ƙabilanci ya kaure a jihar Filato, Sojoji sun shiga tsakani

“Na baiwa shugaba Buhariu bahasi kan ayyukan NNPC tare da rassansa, sa’annan na bayyana masa matakan da muke dauka na samar da isashshen mai a kasa da kuma hakan danyen mai, da suaransu.” Inji Baru

“Awanni 2 muka kwashe da Buhari muna tattaunawa” – shugaban NNPC

Maikanti Baru

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Baru na fadin “Mun tattauna batutuwa da dama da shugaba Buhari, kamar yadda kuka gani, sama da awanni 2 na kwashe tare da shi. Ya gamsu da kokarin da muke yi, kuma ya shawarce mu da mu cigaba da hakan, idan kuma muna bukatar taimakonsa, to kofa a bude take.”

Baru ya bayyana ma majiyar NAIJ.com cewar sakamakon daidaton da aka samu, yanzu kasar na fitar da gangar mai miliyan 2 a kowane rana, daga karshe ta tabbatar da cewar NNPC ba zata kara kudin mai ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli ra'ayin yan Najeriya game da rashin lafiyar Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel