Gwamnan Kano yace ba barci yake yi ba, kasaƙe yake yi

Gwamnan Kano yace ba barci yake yi ba, kasaƙe yake yi

-Gwamna Abdullahi Ganduje ya musanta zargin barci a bainar jama'a da ake yi masa

-Gwamnan yace wannan yarfen siyasa ne kawai, saboda likimo yake yi ba barci ba

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje yace duk surutun da yan hamayya suke yi na cewa baya aiki, sai dai barci, ko a jikinsa. Inji rahoton Daily Trust.

Majiyar NAIJ.com ta shaida cewa Ganduje ya bayyana haka ne yayin dayake ganawa da kungiyar kwadago a ranar ma’aikata na duniya a fadar gwamnatin jihar.

KU KARANTA: Rikicin ƙabilanci ya kaure a jihar Filato, Sojoji sun shiga tsakani

“Yan adawa suna korafin wai ina barci a yayin taruka, ina so sun gane bambamci tsakanin abu guda biyu, ni bana damuwa da yarfen siyasa, don kuwa na saba, ba tun yau ba. Kuma zan cigaba da aikace aikace na”

Gwamnan Kano yace ba barci yake yi ba, kasaƙe yake yi

Gwamnan Kano Ganduje yana Likimo

Gwamna Ganduje yace zai dage wajen ganin ya cigaba da kawo al’amuran cigaba a dukkanin fadin jihar don amfanin al’umma.

Gwamnan Kano yace ba barci yake yi ba, kasaƙe yake yi

Likimo

A wani hannun kuma, gwamnonin Arewa sun sulhunta tsakanin gwamnan jihar Kano da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II sakamakon yakin sunkuru da suka fara, tun bayan wasu kalamai da Sarkin ya furta.

Gwamnonin sun hada da Aminu Waziri Tambuwal, Nasiru El-Rufa’i, Kashim Shettima, Aminu Masari da Abubakar Sani Bello.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan siyasa ne baya sata?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel