Hukumar sojin sama tayi luguden wuta kan yan Boko Haram

Hukumar sojin sama tayi luguden wuta kan yan Boko Haram

-Rundunar NAF tayiwa Boko Haram wutan sama

-Tace ta kasha kwamandojinta da dama a wannan mumunan hari

Hukumar sojin saman Najeriyan Operation “LAFIYA DOLE” tace ta fitittiki taruwan wasu yan Boko Haram a wani sashen yankin arewa maso gabas.

Hukumar sojin saman tace ta kai wata harin jirgin sama inda ta tarwatsa taruwan yan Boko Harama wata kauyen Mangosum, jihar Borno.

Diraktan yada labaran hukumar sojin saman, Air Commodore Olatokunbo Adesanya, ya bayyana wannan ne a wata jawabin da yya bayar ranan Talata a Abuja.

Air Commodore Olatokunbo Adesanya, yace hukumar ta taimakwa rundunar 27 Task Force Battalion wajen fitittikan yan ta’addan.

Hukumar sojin sama tayi luguden wuta kan yan Boko Haram

Hukumar sojin sama tayi luguden wuta kan yan Boko Haram

Game da cewarsa, sashen ilimin leken asirin hukumar sojin saman ta bibiyi wasu yan tsirarun Boko Haram da suka kai hari kan bataliyan zuwa wata kauye a Mangosum.

“Bisa ga harin da hukumar NAF ta kai da jirgin Alpha Jets da F-7Ni, sakamakon farmaki ya nuna cewa an hallaka wasu shugabannin Boko Haram inda suka taru tare da mabiyansu.”

KU KARANTA: Aisha Buhari tayi magana kan jikin Buhari

“Kana kuma an lalata makamai tare da wasu kayayyakin a harin mai kyau,”.

Diraktan yada labaran yace ai hallakasu ne yayinda suke kokarin sake kafa daba a Sambisa.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel