Da yiwuwan Buhari ya koma Landan wannan ranan - Majiya

Da yiwuwan Buhari ya koma Landan wannan ranan - Majiya

- Ana zargin cewa wasu na wasa da lafiyan shugaba Buhari

- Majiya a fadar Aso Villa ta fadi ranan da zai koma kasar Ingila

Jaridar Sahara Reporters ta bada rahoton cewa kawai an fito da shugaban kasa office jiya Talata, 2 ga watan Mayu ne saboda rage magnaganun jama’a kan rashin lafiyan Buhari.

Sahara Reporters ta kara da cewa shugaba Buhari ya shiga ofishinsa a yau cikin gajiya da alamun rashin karfi domin ganawa da dirakta manajan babban kamfanin ma feturin Najeriya, Maikanti Baru da ministan shari’a, Abubakar Malami.

Shugaba Buhari bai yi Magana da manema labarai bayan ganawar ba.

Da yiwuwan Buhari ya koma Landan wannan ranan - Majiya

Da yiwuwan Buhari ya koma Landan wannan ranan - Majiya

Amma NAIJ.com bata samu dalilin ganawa da mutane 2 kacal da shugaba Buhari yayi ba.

An kara da cewa uwargidansa na son ya koma wajen likitocinsa a Ingila domin cigaba da jinya domin samun cikakken lafiya.

KU KARANTA: Likitoci sun tafi yajin aiki a Kogi

Majiyar ta kara da cewa Aisha c eke kula da shugaba Buhari yanzu bayan yaranshi mata, Halima da Zahra, sun kasance masu kula da shi.

Kana kuma majiyar ta bayyana sabon rahoton cewa shugaba Buhari zai koma Landan ranan 10 ga watan Mayu, domin cigaba da jinya.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel