Likitoci za su shiga wani yajin aiki

Likitoci za su shiga wani yajin aiki

– Likitocin Jihar Kogi na shirin shiga wani yajin aiki

– A daren yau Laraba za a tafi yajin aikin

– Kungiyar Likitoci watau NMA ta tabbatar da wannan

NAIJ.com na samun labari cewa Likitocin Jihar Kogi za su tafi yajin aiki.

Za a shiga yajin ne a daren Larabar Yau.

Haka dai Kungiyar NMA ta Likitocin kasar ta bayyana.

Likitoci za su shiga wani yajin aiki

Likitoci na duba wani maras lafiya

Bangaren Kungiyar Likitocin Najeriya watau NMA na Jihar Kogi ta umarci ‘Ya ‘yan ta da su shiga wani yajin aiki na sai-baba-ta-gani daga tsakiyar daren yau saboda wasu kudin su da su ka makale ba a biya su ba har fiye da shekara guda.

KU KARANTA: Dubi yadda Shugaba Buhari ya koma

Likitoci za su shiga wani yajin aiki

Likitocin Jihar Kogi za su tafi yajin aiki

Likitocin dai za su tafi yajin ne a dalilin wasu bashi da su ke bin Jihar har yanzu kuma babu labari. Shugaban Kungiyar Likitocin Jihar Dr. Tijjani Godwin da kuma Sakataren sa Dr. Zubairu Kabiru su ka ce ya zama dole bayan wani taro da aka yi na gaggawa.

Likitocin sun ce lallai Gwamnan Jihar ya ba su kunya duk da an dauki dogon lokaci domin a sasanta amma abu ya faskara. A Najeriya ma ana kishin-kishin din cewa shugaba Buhari zai koma wajen Likitoci mako mai zuwa.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dubi yadda wata 'Yar Najeriya ke kida

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel