2019: Fostocin takarar shugaba Buhari sun fara yawo a gari

2019: Fostocin takarar shugaba Buhari sun fara yawo a gari

– Shugaban kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin lafiya

– Duk da haka sai ga fostocin shugaban kasar an gani a Birnin Tarayya

– Shin shugaba Buhari zai fito takar ne a zaben 2019?

Ana ta rade-radin cewa jikin Shugaba Buhari kullum kara tabarbarewa yake yi

Fadar shugaban kasar ta karyata wannan tace umarni na Likitoci yake bi shi yasa ya boye.

Yanzu dai an tsinci wasu hotunan takarar shugaba Buhari a zabe mai zuwa a Birnin Abuja.

2019: Fostocin takarar shugaba Buhari sun fara yawo a gari

Fostocin Buhari sun fara yawo

Ganin rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari har wasu na kira ya mika mulkin ko ya koma asibiti domin Likitoci su duba sa sai kuma ga shi ana ganin hotunan takarar sa na zabe mai zuwa a 2019.

KU KARANTA: Dubi yadda Buhari ya canza gaba daya

2019: Fostocin takarar shugaba Buhari sun fara yawo a gari

Shugaba Buhari da mataimakin sa Osinbajo

Kwanan nan Ministan sufuri kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi ya bayyana cewa idan har shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya takara a zabe mai zuwa to ba shakka yana bayan sa.

Matar shugaban kasar Hajiya Aisha Buhari ta godewa ‘Yan Najeriya da addu’o’in da ake yi wa Mai gidan na ta. Aisha Buhari tace rashin lafiyar ba ta kai inda ake tunani ba kuma asali ma yana aikin sa har yanzu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za a raba kasar nan ne?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel