Yau za ayi ta ta kare: Osinbajo da su Babachir

Yau za ayi ta ta kare: Osinbajo da su Babachir

– Yau ake sa ran kammala binciken shugaban Hukumar NIA da aka dakatar

– Haka kuma an binciki Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal

– Shugaban kasa ya nada Mataimakin sa ya binciki zargin

Yau ake sa ran a karkare binciken da ake yi game da Babachir David Lawal.

Ana kuma binciken shugaban Hukumar NIA na kasa.

Jiya, Talata, 2 ga watan Mayu dai mu ka bayyana maku cewa da alamu allura ta tono garma a binciken.

Yau za ayi ta ta kare: Osinbajo da su Babachir

An dakatar da Mr. Babachir David Lawal

Kamar yadda aka sani ana ta bincike game da Ambasada Ayo Oke shugaban Hukumar da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal bayan an dakatar da su. Mataimakin shugaban kasa da kuma Ministan shari’a da mai bada shawara kan harkar tsaro ne aka sa wannan aiki.

KU KARANTA: Allura ta tono garma a binciken Babachir

Yau za ayi ta ta kare: Osinbajo da su Babachir

Babachir: Ba mamaki Shugaba Buhari zai gana da Osinbajo

Yau ake dai sa ran za a kammala wannan aiki a mikawa shugaban kasar rahoto bayan an cika makonni biyu da aka bada. Shugaba Buhari dai ya bada umarni a hukunta duk wanda aka samu da rashin gaskiya ko wane ne.

Ba mamaki dai binciken ya kara jefa wasu Jama’a cikin matsala don tun kwanaki mun samu labari an fara mika wasu zuwa ga Hukumar EFCC. Ana zargin Babachir da saba ka’idoji wajen bada kwangiloli kuma ba mamaki ta shi ta kare.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An saki Nnamdi Kanu na Biyafara daga Kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel