Warin kaji na iya korar jinsin sauro mai sanya cutar maleriya

Warin kaji na iya korar jinsin sauro mai sanya cutar maleriya

- Bincike ta nuna cewa kaza na daya daga cikin halittun da sauro ke gudu

- Masana sun kuma gano cewa akwai jinsunan sauro da dama wadanda sun tsani warin kaji

- Masanan na son su gwada ko za a iya samar da wani abu mai warin kaza da zai iya korar jinsin sauro daga gidaje

Masu bincike daga kasar Sweden sun gano cewa daya daga cikin halittun da sauro yake gudunsu shine kaza, abinda ke nunin cewa watakila kwanciya kusa da kaza na iya kare mutum daga cizon sauro.

Ga al'ummar dake zaune a kasashen bakar fata na Afirka, kwanciya ko yin barci a kusa da inda kaji suke ba wani bakon abu ba ne, musamman a yankunan karkara.

Masana sun gano cewa akwai jinsunan sauro da dama wadanda sun tsani warin kaji, abinda ke nufin cewa watakila za a iya samo wata hanya mai sauki ta yin rigakafin cutar maleriya da sauron ke haddasawa.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, akasarin sauro, ciki har da wadanda ke dauke da kwayar cutar maleriya, su na cizon mutane, su sanya musu cutar ta hanyar zuba musu jinin da suka dauko mai dauke da kwayar cutar.

Amma ba mutane kawai sauron suke cizo ba, su na cizon shanu, awaki da raguna. Amma kuma ba kowace irin dabba suke cizo ba, kamar yadda masu bincike na kasar Sweden suka gano.

Masanan sun kafa tarakka domin kama sauro a wasu gidaje guda 11 a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia, domin neman wani jinsin sauro da ya fi yawa a wurin, watau Anopheles arabiensis.

Daga nan sai masanan suka gwada jinin dake jikin wadannan sauro, inda suka gano jinin dabbobi da yawa, amma kusan dabbar da babu jininta a jikinsu ita ce kaza, duk da cewa kaji su na da yawa a wurin.

Daga nan sai wani farfesa mai suna Rickert Ignell na Jami'ar Kimiyyar Aikin Gona ta kasar Sweden ya roki mutane 11 a wadannan gidaje 11 da su rika kwana a cikin gidan sauron da ba a sanya masa wani magani ba, amma kuma a kusa da shi an sanya wani abu mai warin kaza. A wani gwajin kuma, kazar aka sanya kusa da gidan sauron.

KU KARANTA KUMA: Matsafa sun aika da wata kurciya mai dauke da asiri jihar Kano

Masanan sun yi mamaki da suka ga cewa yawan sauron da suka kama a wannan wurin ya ragu da kashi 95 cikin 100 daga wuraren da babu warin kaza ko kuma kaji a kusa.

Yanzu dai masanan suna son su gwada ko za a iya samar da wani abu mai warin kaza da za a rika kunnawa kamar kyandir domin korar sauro daga gidaje.

An wallafa sakamakon wannan binciken ne a wata mujalla mai suna "Malaria Journal."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga-zangar manoma a Lagos kan mambobinsu da aka yi garkuwa da su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel