Obasanjo ya tsine ma duk masu yi ma gwamantin Buhari zagon ƙasa

Obasanjo ya tsine ma duk masu yi ma gwamantin Buhari zagon ƙasa

-Cif Olusegun Obasanjo ya koka kan yadda wasu keyi ma tattalin arzikin Najeriya zagon kasa

-Obasanjo yayi tsinuwa ga masu yin wannan mugun aiki ko da ba yan Najeriya bane

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tsine ma duk wasu yan Najeriya da yan kasashen waje da ake hada baki dasu wajen yi ma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa musamman a bangaren tattalin arzikin kasa.

Obasanjo ya nuna bacin ransa ne yayin wani taro da kwararrun yan kasar Indiya mazauna Najeriya a garin Abekuta na jihar Ogun, inda ya koka kan shigo kayayyaki marasa inganci Najeriya.

KU KARANTA: An yi gudun famfalaki yayin da wata gawa tayi wuf! ta kamo hannu dan uwanta a Filato

Obasanjo yace “Akwai yan India a Najeriya dake yin abin alheri, muna da wasu ma a nan Abekuta. Amma akwai wasu miyagun yan India dake yi ma tattalin arzikin Najeriya zagon kasa. A zamani na sai da fitar da da wasu yan kasar India daga Najeriya, amma Yar’adua da Jonathan suka dawo dasu.

Obasanjo ya tsine ma duk masu yi ma gwamantin Buhari zagon ƙasa

Obasanjo

“Amma daga bisani sun ma sun fitar dasu daga kasar nan, kasan abinda da mai hali, baya canja halinsa, a ganin su zasu iya bada cin hanci a ko ina a Najeriya.

“Don haka tsinuwa ta tabbata akan duk wani dan Najeriya ko wanda ba dan Najeriya ba dake ganin zai lalata mana kasa, zan yi amfani da iko na na ganin mun dakatar da irin wannan halayya.

“Ya za’a yi ace ana girka dafa duka ana shigo da shi Najeriya ana siyarwa, wani irin lalacewa ne wannan? Ba zamu yar da wannan ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin tattalin arzikin kasa ya habaka?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel