Ra’ayi: Wace cuta ke damun shugaba Buhari?

Ra’ayi: Wace cuta ke damun shugaba Buhari?

– Fadar shugaban kasa ta saba cewa babu abin damuwa game da rashin lafiyar Buhari

– Ana rade-radin cewa rashin lafiyar na kara jagwalgwalewa

– Ta kai har wasu na cewa ba ya iya cin abinci

Sanannen abu ne cewa har ya zuwa wannan farkon watan Mayu shugaba Buhari bai da lafiya.

Wasu na fadin cewa ma da bututu yake samu ya cin abinci.

Fadar shugaban kasar tace sam ba haka bane inda har ya leka Ofis a Ranar Talata

Ra’ayi: Wace cuta ke damun shugaba Buhari?

Shugaba Buhari bai da lafiya

Kowa ya san shugaba Buhari mutum ne mai koshin lafiya matuka wanda yake fara aiki tun farkon safiya. Ko farkon hawan sa yayi ta zirga-zirga kasa zuwa kasa daga baya kuma sai ya fara daga kafa har ta kai ya gaza zuwa Garin Ogoni a Yankin Neja-Delta.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya leka Ofis

Ra’ayi: Wace cuta ke damun shugaba Buhari?

Shugaba Buhari zai bar Najeriya kwanakin baya

Zuwa farkon makon nan na Watan Mayu Jama’a na cikin damuwa ganin cewa ko ganin shugaban ba ayi. Don kuwa ya dauki kusan makonni 3 bai hallarci taron Majalisar zartarwa ba. Kai ko Sallar Juma’a bai samu zuwa ba balle daurin auren wani na kusa da shi Yusuf Sabi’u.

Wasu masu maganganu haka kurum su na ganin cewa cutar da shugaban kasar aka yi duk da ya karyata hakan. Sai dai sanin kowa ne cewa yayi muguwar rashin lafiya inda ya je har Landan. Jama’a na mamakin yadda shugabannin Yanki guda ne kurum ke fama da rashin lafiya a Ofis.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wanda ya fi kowa tsawo a Duniya dan Najeriya ne?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel