‘Yan Najeriya na zargin Buhari da boye halin lafiyarsa

‘Yan Najeriya na zargin Buhari da boye halin lafiyarsa

- ‘Yan Najeriya na zargin shugaban kasar Muhammadu Buhari da boye yanayin lafiyarsa

- Sun koka kan yadda gwamnatin kasar ta fitar da bayanai kadan game da lafiyar shugaaban

- Suna masu fatan shugaban ba zai mutu kan karagar mulki ba

Ana zargin shugaba Muhammadu Buhari da boye yanayin lafiyarsa kamar yadda takwaransa na Amurka, Donald Trump, ya ɓoye adadin harajinsa.

'Yan Najeriya suna kara damuwa game da lafiyar shugaba Buhari, suna masu fatan shugaban ba zai mutu kan karagar mulki ba, kamar yadda shugaba Umaru Musa 'Yar'Adua ya rasu a shekarar 2010 bayan doguwar rashin lafiya wadda ta sa ya je neman magani a kasar Jamus da Saudiyya.

Rashin halartar Buhari zaman majalisar ministoci biyu a jere da kuma rashin zuwa masallacin Juma'ar da ke da nisan minti daya daga ofishi da gidansa sun ruruta damuwar a baya-bayan nan.

‘Yan Najeriya na zargin Buhari da boye halin lafiyarsa

Shugaba Buhari na gaisawa da gwamnan jihar Kaduna mallam Nasir El-Rufai bayan sallah juma'a

KU KARANTA KUMA: Rayuwa ! Kalli hotunan Buhari lokacin ya hau mulki da yanzu

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, gwamnatin kasar ta fitar da bayanai kadan game da lafiyarsa, kuma babban jami'in tsaron shugaban kasa ya kori wani dan jarida da ke aiki a daya daga cikin manyan jaridun kasar bayan ya rubuta labari kan damuwar ta baya-bayan nan.

Masu taimaka wa Buhari kan watsa labarai sun nisanta kansu daga matakin da jami'in ya dauka, kuma sun sa wani babban jami'i ya soke korar da aka yi wa dan jaridar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali amsa da wani mutun ya bayar kan ko da gaske ne shugaba Buhari ya kubutar da Najeriya daga koma bayan tattalin arziki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dubi jerin hanyoyi da gadoji da gwamnatin APC ta ce ta kammala cikin shekaru 2

Dubi jerin hanyoyi da gadoji da gwamnatin APC ta ce ta kammala cikin shekaru 2

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel