Shehu Sani ga El-Rufai “Idan kana Real Madrid ne, ni ina Barcelona”

Shehu Sani ga El-Rufai “Idan kana Real Madrid ne, ni ina Barcelona”

-Kwamared Shehu Sani yayi bakin babu wanda ya isa ya hana shi tsayawa takara a 2019

-Magoya bayan Kwamared sun bukaci ya fito takarar gwamnan jihar Kaduna

Rikicin siyasan jihar Kaduna ya dauki wani sabon salo, musamman na cikin gidan jam’iyyar APC inda aka jiyo sanatan Kaduna ta tsakiya kwamared Shehu Sani yana kumfar baki yana fadin za’a fafata da shi a zabukan shekarar 2019.

Shehu Sani ya bayyana haka ne a ranar Litinin 1 ga watan Mayu lokacin daya karbi bakoncin wasu magoya bayansa dake garin Jere, inda suka kawo amsa ziyara, kamar yadda gidan rediyon Freedom ta ruwaito.

KU KARANTA: An samu sabuwar tawariyya a cikin jam’iyyar PDP

Magoya bayan nasa sun yi korafin cewa sun sanya hoton sanatan a garinsu, amma wasu wadanda basu son zaman lafiya sun cire kuma sun kalubalance su dasu kai kara duk inda zasu iya kaiwa, ba abinda zai faru, inji majiyar NAIJ.com.

Shehu Sani ga El-Rufai “Idan kana Real Madrid ne, ni ina Barcelona”

Sanata Shehu Sani

Dayake nasa jawabin, Sanata Shehu Sani ya gode ma magoya bayan nasa, tare da jinjina musu kan hakurin da sukeyi, sa’annan ya tabbatar musu da cewa babu wanda ya isa ya hana shi takara a shekarar 2019, don kuwa shi dank are hakkin biladama ne, don haka ya saba rigima.

“Na fada na kara, babu wanda ya isa ya hana tsayawa takara a shekarar 2019, kowanene kuwa. Mutum ya bar ganin zai kada ni a zaben cikin gida, toh ya sani, idan yana Real Madrid, toh ina Barcelona, idan kuma yana Barcelona, ina Man U. sai dai mu hadu final.” Inji Shehu Sani.

Dama dai magoya bayan kwamared Shehu Sani sun dade suna kira a gare shi da ya nemi takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna, don a ganin su shi yafi dacewa da tafiyar da al’ummar jihar yadda ya kamata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani hukunci ya dace da barayin gwamnati?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel