Sarkin Kano ya shawarci gwamnati ta fara tatsan kowane mutum a Kano naira 1000

Sarkin Kano ya shawarci gwamnati ta fara tatsan kowane mutum a Kano naira 1000

-Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya baiwa gwamnatin jihar Kano shawarar yadda zata habbaka kudaden shigarta

-Gwamna Ganduje yace zasu yi amfani da kudin wajen gina sabbin hanyoyi da kulawa da tsofaffin

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya shawarci gwamnatin jihar Kano data fara karban harajin naira dubu daya daya daga hannun kowane mutumin mazaunin jihar Kano don ta habbaka hanyoyin samun kudin shigarta.

Sarkin ya bayyana haka ne a ranar Lahadi 30 ga watan Afrilu yayin wani taron tattaunawa akan wata sabuwar dokar karbar haraji a hannun motocin haya a jihar Kano da gwamnati ke son samarwa.

KU KARANTA: An samu sabuwar tawariyya a cikin jam’iyyar PDP

Sarkin yace duba da yawan al’ummar jihar Kano da suka kai miliyan 12, idan kowa zai biya 1000 a kowane wata, jihar zata samu naira biliyan 12 kenan kowane wata.

Sarkin Kano ya shawarci gwamnati ta fara tatsan kowane mutum a Kano naira 1000

Sarkin Kano

NAIJ.com ta ruwaito “karban kudi kalilan daga jama’a dayawa, yafi sauki, kuma zai habbaka ma gwamnati kudaden shiga. Ta hanyar biyan haraji ne kadai zamu kare mutuncin mu. Ana zagin mu ne saboda mun dogara kacokam da kudin man fetur.” Inji shi.

Sa’annan Sarki ya shawarci gwamnati data tabbata masu manyan gidaje da filaye a unguwannin masu kudi suna biyan harajin gidaje da filaye yadda ya kamata, daga karshe yace masarautar Kano tana goyon bayan gwamnatin jihar dari bisa dari.

A nasa jawabin, Ganduje yayi bayani cewa “Harajin da muke fatan mu fara karba zai taimaka mana wajen gyaran hanyoyin mu, tare da bamu damar gina sabbin hanyoyi. Sa’annan kudaden zasu bamu isashshen daman gina asibitoci da makarantu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli maganan da Sarki Sunusi yayi daya tada hazo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel