Obasanjo, Abdulsalam da Babangida sun yi wata ganawar sirri a Minna

Obasanjo, Abdulsalam da Babangida sun yi wata ganawar sirri a Minna

-Abdulsalam, Obasanjo da IBB sun sa labule a gidan IBB dake Minna

-An dakatar da kowa daga shiga gidan IBB har sai da suka kammala ganawar tasu

Tsoffin shuwagabannin kasar Najeriya kuma dattijai masu fada a ji a kasar nan, Obasanjo, Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalam Abubakar sun gadanar da wata tattaunawa a gidan IBB dake kan dutse a Minna.

Manyan mutanen sun gana ne a gidan IBB a ranar Litinin 1 ga watan Mayu, NAIJ.com ta ruwaito cewa tsoffin shugabannin sun kwahse kusan awanni biyu suna tattaunawa a tsakaninsu.

KU KARANTA: Koken Albashi ya mamaye ranar ma'aikata ta duniya

Sai dai ba’a san tabbataccen makasudin gudanar da wannan taro ba, sai dai bincike ya nuna cewa ba ya rasa nasaba da al'amuran da suka jibanci kasa.

Obasanjo, Abdulsalam da Babangida sun yi wata ganawar sirri a Minna

Obasanjo, Abdulsalam da Buhari

Jaridar Leadership ta ruwaito cewar har sai da aka dakatar da baki dake yawan kai ziyara ga IBB gidan nasa, gab da isowar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Gwamnan jihar Abubakar Bello ne ya tarbi Obasanjo a filin sauka da tashin jirage na jihar Neja, daga nan kuma ya raka shi har gidan IBB, bayan nan sai ya fita ta kama gabansa.

Saboda tsananin muhimmancin wannan ganawa ta manyan kasa, hatta hadiman IBB na kud da kud dake tare da shi a kullum, sai da aka sallame su, kafin a fara taron.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sarki Sunusi ya caccaki shuwagabannin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel