LABARI DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari ya koma bakin aikinsa

LABARI DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari ya koma bakin aikinsa

- Shugaba Muhammadu Buhari ya koma bakin aiki bayan da ya shafa kusan mako biyu a gida

- Bashir Ahmad ya bayyana cewa shugaba Buhari ya koma bakin aikinsa ne yau Talata, 2 ga watan Mayu

Bayan wasu kwanakin hutu da ya dauka daga ofishin, shugaba Muhammadu Buhari ya koma bakin aiki.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, mai taimakawa shugaban kasa a kan sabon kafofin watsa labarai, Bashir Ahmad ya bayyana cewa shugaba Buhari ya koma bakin aikinsa a ranar Talata, 2 ga watan Mayu. Ya yi wannan bayani ne a wata sanarwar wanda ya wallafa kan shafinsa na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi alkawari ga ma’aikata kan albashinsu

A cewar shi, shugaban kasar Buhari ya karbi ziyarar da kuma sauraren jawabi daga shugaban NNPC, Maikanti Baru.

LABARI DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari ya koma bakin aikinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ya kuma saurari jawabi daga ministan shari'a, Abubakar Malami SAN.

Za a iya tuna cewa kusan mako biyu kenan rabon da a ga shugaba Buhari a bainar jama'a, abin da yasa 'yan kasar ke tambayar ko'ina shugaban yake ta hanyar amfani da maudu'in #WhereIsBuhari a shafin Twitter.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel