Sule Lamido yana fuskanta shari’a a Dutse, babban birnin jihar Jigawa

Sule Lamido yana fuskanta shari’a a Dutse, babban birnin jihar Jigawa

- An tafi da tsararren tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido Dutse, wato babban birnin jihar domin fuskantar hukunci sakamakon furucin da yayi na rashin ladabi

- Yan sandar zone 1 ta tsare tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Lamido a Asabar din da ta wuce biyowa bayan korafi da gwamnatin jihar Jigawa tayi

Majiya daga jami’an tsaro a zone 1 sun fadawa NAIJ.com cewa yansanda daukeda manya-manyan makamai ne suka raka dan gaban goshin PDP a tafiyar kimanin awa daya a motar Toyota Hilux zuwa makwantarsa a babban birnin jihar.

Wani daga jami’an tsaron a tafiyar tasu zuwa dutse ya sirrantawa Naij.com akan yarjejeniyar kar a fadi sunansa cewa sun bar kano zuwa dutse a kimanin karfe 5.30 na safe.

KU KARANTA: 2019: Gwamnonin Jihohi 4 da sai sun yi da gaske

Ya kara da cewa a yanzu haka da nake maganar nan muna dutse domin tsaretsaren daya dace ta kara gano cewa an tsinkayar das u jami’an tsaron cewa magoya bayan shi tsohon gwamnan na iya tada zangazanga.

Sule Lamido yana fuskanta shari’a a Dutse, babban birnin jihar Jigawa

Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa

A tabbatar da hakan wakilin yansandan Zone 1, Sambo Dasuki yace, Lamido na Dutse ne domin fuskantar tuhuma.

Akwai rade-raden take cewa wanda wani tsohon gwamnan yana da aniyyar tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2019.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon shugaban kungiyar IPOB

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel