Koken Albashi ya mamaye ranar ma'aikata ta duniya

Koken Albashi ya mamaye ranar ma'aikata ta duniya

-Ma'aikata a Najeriya sun yi bikin ranar ma'aikata cikin rashin samun albashi

-Ma'aikatan sun koka kan karancin albashin da ake biyansu na N18,000, inda suka bukaci a fara biyansu N56,000

Jiya Litinin daya ga watan Mayu ita ce ranar ma’aikata ta duniya, ranar da ta samo asali kimanin shekaru 131 da suka gabata.

A ranar kan yi nazari tare da yin dubi a game da matsalolin da ma’aikata a karkashin gwamnatoci ko kuma kamfanoni masu zaman kansu ke cin karo da su a rayuwa, sa’annan kuma a yi duba ga taimakon da suke baiwa al’umma gaba ki daya.

KU KARANTA: Murnar ranar ma’aikata: An yi ma Saraki, Dogara da Minista ihun ɓarayi (Bidiyo)

Rahoton gidan rediyon Faransa ya bayyana cewar a Najeriya dai batun karin kudin albashi shi ne babban abin da ma’aikata ke bukata daga gwamnati, kamar dai yadda shugabanni kungiyoyin ma’aikatan kasar suka jimma suna koke a kai.

Koken Albashi ya mamaye ranar ma'aikata ta duniya

Ma'ikatana Najeriya

Sakatare-Janar na kungiyar Kwadago a kasar Peter Ozon-Eson ya ce Naira dubu 18 a mastayin albashi mafi karanci babu inda zai kai ma’aikaci.

Ozon-Eson yace “Rashin albashi mai tsoka na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar ma’aikata.”

Sakataren Kungiyar Kwadagon ya cigaba da fadin ma’aikata za su kalubalanci Gwamnonin jihohi da suka ki biyan dimbin ma’aikatansu albashi na tsawon watanni.

A wani hannun kuma, NAIJ.com ta ruwaito ma’aikatan gwamnatin tarayya basu samu albashinsu na watan Afrilu ba har zuwa yau 2 ga watan Mayu, a matakin jiha ma, daddeku ne suka iya biyan albashin watan Afrilun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Najeriya sun koka kan tsadar rayuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel