Ma'aikatan jihar Filato sun gamsu da yadda gwamnati ke biyansu a kan kari

Ma'aikatan jihar Filato sun gamsu da yadda gwamnati ke biyansu a kan kari

- Ma'aikatan jihar Filato sun bayyana gamsuwarsu yadda gwamnatin jihar ke biyansu albashin su a kan kari

- Gwamnan jihar Filato ya ce hakkin gwamnati ne ta kula da ma'aikatansu domin al'umma su samu yin walwala

Yayinda wasu ma'aikata ke korafi akan rashin biyansu albashi a kan lokaci su kuwa na jihar Filato yabawa gwamnatin jihar suka yi a ranar bikin ma'akata ta duniya a ranar Litini, 1 ga watan Mayu.

Ma'aikatan jihar Filato sun bayyana gamsuwarsu da tsare tsaren da gwamnatin jihar ta kirkiro na biyansu hakkokinsu akan lokaci.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, a wani kasaitatcen taro da ma'aikatan suka gudanar domin tunawa da ranar ma'aikata ta duniya shugaban kungiyar ma'aikatan Kwamrade Jibrin Banchir ya ce gwamnatin jihar tana biyan ma'aikata albashinsu akan kari.

Ma'aikatan jihar Filato sun gamsu da yadda gwamnati ke biyansu a kan kari

Ma'aikatan jihar Filato a filin bikin ranar ma'aikata

Yana mai cewa babu abun da zasu ce sai godiya ga Allah domin sun dade basu yi irin wannan bikin ba. Ya ce cikin shekaru biyu da zuwan wannan gwamnatin ana biyansu albashi da fansho a bisa kaida.

Duk da cewa gwamnatin na biyan albashin a kan kari har yanzu akwai wasu kudaden da gwamnatin bata biya ba kamar mafi kankantan albashin matakin farko a kananan hukumomi da sauran kudin hutu da kuma kudin fanshon wadanda suka bar aiki kwana kwanan nan.

Jibrin ya ce sun gane cewa ba fitina ba ce zata biya masu bukata. Irin shawarwari da su keyi da gwamnati ne zasu dinga kaisu samun nasara.

KU KARANTA KUMA: Kamata yayi a maida albashi mafi karanci N145,000 - Sanata Shehu Sani

Sakataren 'yan fansho na jihar, Bulus Ibrahim ya ce matsalolinsu sun ragu matuka in bar da batun kudin sallama.

Shi ma gwamnan jihar ya ce hakkinsu ne su kula da ma'aikatansu domin al'umma su samu yin walwala. Gwamna Lalong ya ce abun da suka ga shugaban kasa na yi ya kamata su yi. A cewarsa shugaban kasa yana farin cikin ya ga an biya ma'aikata akan lokaci.

Ya ce biyan albashi ya kawo zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali inda wata ma'aikaciyar LAWMA mai shekaru 60 da haihuwa ke korafi kan rashin biya albashi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel