Rashin lafiyar shugaban kasa: Babu dalilin tada hankali

Rashin lafiyar shugaban kasa: Babu dalilin tada hankali

– Fadar shugaban kasa ta kara magana game da rashin lafiyar Buhari

– Ana rade-radin cewa jikin sa kullum kara tabarbarewa yake yi

– Sai dai Fadar tace umarni ne kurum na Likitoci yake bi

Farkon makon nan NAIJ.com ta samu labarin cewa rashin lafiyar shugaban kasa tayi kamari.

Jaridar nan ta Sahara Reporters ta fadi wannan labari.

Fadar shugaban kasar tace sam ba haka bane.

Rashin lafiyar shugaban kasa: Babu dalilin tada hankali

Babu dalilin tada hankali game da rashin lafiyar shugaba Buhari

Fadar shugaban kasa ta kara jaddada cewa rashin lafiyar shugaba Buhari ba abin tada hankali bane. Fadar ke cewa Likitoci ne su ka ba shugaban kasar shawara ya cigaba da hutawa kamar yadda muka samu rahoto.

KU KARANTA: Buhari ya jinjinawa Ma'aikatan Najeriya

Rashin lafiyar shugaban kasa: Babu dalilin tada hankali

Shugaban kasa tare da Mataimakin sa

Wani cikin masu aiki tare da shugaban kasar ya tabbatar da wannan ganin cewa ba a ga shugaban a taron Ranar Ma’aikata ta kasa ba. Aka kara da cewa dai idan har shugaban kasar zai yi tafiya kasar waje zuwa asibiti za a sanar da mutanen kasar.

Makonni fiye da uku kenan ba a ga shugaban kasar bai halarci taron FEC da aka saba yi ba. Sannan kuma bai halarcin daurin auren mai taimaka masa wajen sha’anin gida Sabiu Yusuf ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya za ayi da barayin Najeriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel