Masu yi wa shugaba Buhari fatar mutuwa, toh, ba zai mutu ba – Inji Olumba

Masu yi wa shugaba Buhari fatar mutuwa, toh, ba zai mutu ba – Inji Olumba

- Shugaban na Brotherhood ya ce shugaba Buhari ba zai mutu yanzu ba kamar yadda wasu ke masa fata

- Shugaban ya ce Allah ya zabo muna shugaba Buhari a matsayin shugaban kasar don ya yaki cin hanci

- Olumba ya shawarci gwamnatin tarayya cewa dole ne ta samar da zaman lafiya da hadin kai a kasar

Shugaban na Brotherhood wadda aka sani da Cross and Star, Mai Tsarki Olumba Olumba Obu ya bayyana cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari ba zai mutu a ofishi ba kamar yadda wasu bata gari ke zato.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Olumba ya bayyana haka ne a Calabar a lokacin da yake jawo hankalin masu yi wa shugaba Buhari addu'a da fatar mutuwa, ya ce Allah ya zabo muna shugaban ne a matsayin shugaban kasa na Najeriya don ya yaƙi cin hanci.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari ya bi shawarar likitoci ya tafi hutun jinya

A cewar Olumba, gwamnatin shugaba Buhari ta yi nasara a yunkurin dawo da wasu kudaden Najeriya da aka sace. Olumba ya shawarci gwamnati cewa dole ne ta samar da zaman lafiya da hadin kai a kasar.

Masu yi wa shugaba Buhari fatar mutuwa, toh, ba zai mutu ba – Inji Olumba

Shugaba Muhammadu Buhari

Olumba ya jaddada cewa: "Dole ne shugaban kasa ya yi addu'a ga Allah domin ya shiryar da shi zuwa yadda zai yi amfani da kudaden da aka gano don amfanin 'yan Najeriya

Ya kara kira ga ‘yan Najeriya da kuma masu zuba jari da su amince da kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali yadda mutanen daura ke murnar dawowar shugaba Buhari daga Landon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel