Shugaba Buhari bazai iya juriyar karin shekaru 4 ba, inji jigon jam’iyyar PDP

Shugaba Buhari bazai iya juriyar karin shekaru 4 ba, inji jigon jam’iyyar PDP

- Tsohon mataimakin shugaba na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kuma tsohon dan takarar gwamnatin jihar Legas, Adedeji Doherty yayi kira zuwaga Jam’iyyar APC da ta manta da tunanin tsayarda shugaba Muhammmadu Buhari a matsayin dan takararta a shekarar 2019

- Doherty yace duk mai cewa Buhari ya fito takarar makiyi ne a garesa ,kuma ya karfafa zancensa da cewa shugaban bazai iya jurewa wasu shekaru hudu ba

Wani jigon jam'iyyar PDP ya kirayi shugaba day a zauna ya lura da lafiyarsa a maimakon yawace-yawacen da wahalhalun siyasa da zaiyi.

Ya sanarwa da NAIJ.com cewa, “Duk wanda ya nemi Buhari da yayi komawa ta biyu makiyi ne a gareshi. Ina kyautata zaton iyalansa zasu so hanashi tsayawa takarar koda kuwa wasu mahandama na neman ingizashi ga hakan domin cinma manufofinsu.

Shugaba Buhari bazai iya juriyar karin shekaru 4 ba, inji jigon jam’iyyar PDP

Cif Adedeji Doherty, jigon jam'iyyar PDP

“Bana zaton Buhari nada cikarkiyar lafiyar da zai iya juriyar badakalar yawace-yawacen siyasa ballantana dadin shekaru hudu nan gaba. Masu fatan janshi ga tsayawa takarar 2019 ba masoyansa bane.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya bi shawarar likitoci ya tafi hutun jinya

“Kuma ba makaunatar Najeriya bane. Yawace-yawacen siyasar neman shugabancin kasa ba karamin abu bane.Buhari kuma ba lalle bane ya iya juriya akan hakan.”

Game da warware wannan matsalar da ta shafi jam’iyyar PDP, Doherty yace jam’iyyar na nan na kokarin hada kan ‘ya’yanta don tunkarar shekarar 2019.

Shugaba Buhari bazai iya juriyar karin shekaru 4 ba, inji jigon jam’iyyar PDP

Shugaba Buhari

“Yawancin yan najeriya basua farin ciki da abinda ke aukuwa a garemu PDP, saboda suna tsammatar mafita daga garemu , da kuma taimakawa da zamuyi domin kwatarda daga bahagon mulkin APC. Shugabancin APC ya gaza.kuma karshensa yazo, a fitowa baro-baro APC ta kai karshenta.

“APC ta gaza cinma bukatun Yan Najeria. Mafi yawancin mutane na cikin yunwa da kunci sakamakon mugun mulkin APC. Akwai yunwa a kasa . rayuwa na wa mafi yawancin. Yan najeriya na Allah-Allah lokacin zaben 2018 da 2019 don daukar fansar rashin kyautawa da rashin cika alkawurran da jam’iyyar APC ta jama’a.'' Inji shi.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan matsin tattalin arziki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel