Ya kamata Buhari ya bi shawarar likitoci ya tafi hutun jinya

Ya kamata Buhari ya bi shawarar likitoci ya tafi hutun jinya

- ‘Yan Najeriya sun shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki hutun jinya domin kula da kansa

- Kusan mako biyu kenan rabon da a ga shugaba Buhari a bainar jama'a sabilin rashin lafiyarsa

- Rashin fitowar shugaba Buhari na jawo fargaba a zukatan wasu 'yan kasar musamman magoya bayansa

Wasu daga manyan kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya dauki hutu domin yin jinyar rashin lafiyar da ke damunsa.

NAIJ.com ta ruwaito cewa rashin bayyanar shugaban a taron majalisar zartarwa sau biyu a jere da kasa halartar sallar Juma'a, wanda yasa ana ta ce-ce-ku-ce a kan rashin lafiyarsa.

A sanarwar da suka fitar, masu fafitikar, da suka hada da lauya Femi Falana, Farfesa Jibrin Ibrahim da Auwal Rafsanjani, sun ce: "Ya zama wajibi a garemu mu bashi shawara ya bi umarnin da likitocinsa suka bashi ta hanyar daukar hutu domin ya kula da lafiyarsa."

Ya kamata Buhari ya bi shawarar likitoci ya tafi hutun jinya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo

Kusan mako biyu kenan rabon da a ga shugaba Buhari a bainar jama'a, abin da yasa 'yan kasar ke tambayar ko'ina shugaban yake ta hanyar amfani da maudu'in #WhereIsBuhari a shafin Twitter.

KU KARANTA KUMA: Rikici a Jam’iyyar APC mai mulki

Wannan kuma ya sa fargaba a zukatan wasu 'yan kasar musamman magoya bayansa, inda wasu rahotanni ke nuna cewa rashin lafiyar tasa ta kara ta'azzara.

Mataimakinsa Yemi Osinbajo ne yake gudanar da yawancin al'amuran gwamnati, kuma wasu na ganin hakan yana kawo tsaiko wurin tafiyar da al'amura.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon dawowar shugaban kasa daga Landon a lokacin da ya tafi hutun duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel