Da dumi dumi : Sule Lamido ya gurfana a kotu

Da dumi dumi : Sule Lamido ya gurfana a kotu

- Sule Lamido ya isa garin Dutse yau Talata domin gurfana gaban kotu

- Jami’an tsaro suna nan shirye saboda wadanda zasuyi niyyan yin zanga-zanga

- Hukumar yan sanda ta damke Lamido ne a ranan Lahadi, 30 ga watan Afrilu akan laifin ziga mabiyansa su tada tarzoma a zaben kananan hukumomin jihar Kano

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa hukumar yan sandan jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, garin Dutse domin gurfana.

Game da cewan rahoton, manyan jami’an tsaro ne suka raka Sule Lamido da safiyar yau Talata, 2 ga watan Mayu.

Jaridar Vanguard ta laburta maganar wata majiya cewa : “ Mun dau hanyan Dutse daga Kano misalin karfe 5:30 na safe, muma a yanzu haka, mun isa Dutse domin gufanar da tsohon gwamnan."

Da dumi dumi : Sule Lamido ya gurfana a kotu

Da dumi dumi : Sule Lamido ya gurfana a kotu

Kakakin hukumar yan sandan yace : “Hakana, za’a gurfanar da Lamido a Dutse.”

KU KARANTA: Yan fansho a Zamfara na cikin mawuyacin hali

NAIJ.com ta tattaro cewa hukumar yan sanda da sauran jami’an tsaro suna shirye da kawar da kowani irin zanga-zangan da mabiya Sule Lamido zasu iya yi.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel