Kunji abunda yan sanda za suyi wa Sule Lamido yau?

Kunji abunda yan sanda za suyi wa Sule Lamido yau?

- Wata majiya a rundunar 'yan sanda ta shiyya ta daya da ke Kano ta shaida wa majiyar ta BBC mu cewa za ta gurfanar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, a gaban kotu, ranar Talata.

- Majiyar ta ce Sule Lamido zai bayyana ne a gaban kuliya a tsohuwar jihar da ya mulka wato Jigawa.

Gwamnatin jihar Jigawa ce dai ta kai koken cewa tsohon gwamnan ya yi kalaman tunzura mutane da ka iya janyo tashin-tashina.

NAIJ.com ta tuna cewa a ranar Lahadi ne dai 'yan sanda suka kai samame gidan Sule Lamido da ke a birnin Kano.

Kuma a ranar ne suka gayyace shi domin bayani kan laifin da ake tuhumar sa da shi.

Kunji abunda yan sanda za suyi wa Sule Lamido yau?

Kunji abunda yan sanda za suyi wa Sule Lamido yau?

KU KARANTA: Kamata yayi a maida albashi mafi karanci N145,000 - Shehu Sani

An dai ce Sule Lamido ya fada wa taron magoya baya cewa "su kasa, su tsare sannan su kuma raka akwatinan zabensu." a zaben kananan hukumomin da ke tafe a jihar.

Wasu magoya bayan Sule Lamido dai na kallon kama tsohon gwamnan da yunkurin toshe bakin masu hamayya.

A baya dai shugaba Buhari ya sha amfani da irin wadannan kalamai a tarukan kamfe na neman zabensa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel