Hukumar EFCC ta damke jami’an soji 2 da suka karkakar da N339m

Hukumar EFCC ta damke jami’an soji 2 da suka karkakar da N339m

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta damke jami’an soji 2 da suka aikata laifin karkatar da N339m na iyakan sojin da suka kwanta dama.

Sauran sojin 2 sun arce kuma ana cikin nemansu. Wadanda aka karkatar da kudadensu sun hallaka ne a yakin Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Game da bincike, an damke hafsoshin da a kwamitin fanshon soja wanda da kunshi wani Wing kwamanda da Laftanan kwamanda. Sauran abokan karkatawan sune manajojin bakin United Bank for Africa (UBA).

An tattaro wannan ne lokacin da masu lissafin UBA suka gano cewa an kwashe wasu makudan kudi ba bisa ga doka ba. sai suka sanar da hukumar EFCC.

Hukumar EFCC ta damke jami’an soji 2 da suka karkakar da N339m

Hukumar EFCC ta damke jami’an soji 2 da suka karkakar da N339m

Wani babban majiya a EFCC yace: “ Mun damke Wing kwamnada da Laftanan kwamanda da kuma wasu guda 4 akan karkatar da kudi N339million na sojin da suka hallaka a fagge fama. Saura 2 da ake nema.”

Kana ma a cikin watanni 2, an cire kudi N339million kuma an turasu cikin asusu 11. An cire kudaden ne a bankuna biyu, N298million da N41million. Masu lissafin bankin sun lura da wannan cire kudin a bankin.

KU KARANTA: Dalilin da yasa MTN ta kori ma'aikata 280

“Yayin binciken, manajoji bankin guda 2 sun amsa laifin cewa sun bude wadannan asusu. Anyi amfani da wasu asusun kwastamomi da abokai wajen karkatar da kudi.

Sauran abubuwan zargi 2 wadanda abokan manajojin ne suna boye yanzu. Amma muna neman su.”

Ba da dadewa ba za’a kama su. Sojin sunyi amanna da cewa sun hada baki da ma’aikatan bankin wajen amfani da asusunsu wajen karkatar da kudi. “

Wannan abu dai bai yi dadi ba, wasu na can suna mutuwa a faggen fama, wasu na Abuja suna satan kudinsu.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel