Dalilin da yasa MTN ta sallami ma’aikata 280

Dalilin da yasa MTN ta sallami ma’aikata 280

- Kamfanin MTN tayi bayani filla-filla kan zancen dakatad da ma’aiktanta 280

- Tace tayi hakan ne saboda samun cigaba kuma ta biyasu gratutinsu

Kamfanin sadarwa ta MTN Nigeria tace ya zama wajibi gareta ta sallami ma’aikatanta 280 saboda tana son sauya ayyukanta zuwa na zamani.

Wani ma’aikacin kamfanin wanda aka sakaye sunansa ya bayyana cewa kamfanin zata dauki sabbin ma’aikatan da zau iya taimaka mata wajen cimma manufarta.

Jaridar NAN ta bayyana ranan Juma’a 28 ga watan Afrilu cewa kamfanin sadarwan ta sallami ma’akatanta 280 a lokacin daya.

Majiyar tace a watan Maris, MTN ta sanar da ma’aikatanta cewa zata sallami wasu daga cikinsu.

Dalilin da yasa MTN ta sallami ma’aikata 280

Dalilin da yasa MTN ta sallami ma’aikata 280

Majiyar tace kamfanin MTN ta bayar da wata da mana mutum yayi murabus da kanshi amma za’a biyashi kudin sakayya.

Amma mutane 200 kacal ne sukayi amfani da wannan dama, sauran 80 din koransu akayi.

Majiyar ta kara da cewa wadanda abin ya shafa wadanda sukayi akalla shekaru 5 suna aiki da kamfanin ne.

KU KARANTA: Farfesa Yemi Osinbajo ya karyata Lai

Kuma an basu kashi 75 cikin 100 na albashinsu na wata na yawan shekarun da sukayi aiki a kamfanin a hade.

“Wadanda sukayi murabis da kansu sun samu kudin sakayyan aikin mako 3 na albashinsu na yawan shekarun da sukayi aiki ga kamfanin.

“Wannan na nufi cewa idan kayi shekaru 5 kana aiki da MTN, za’a biya ka kasha 75 cikin 100 na dukkan albashi da ka karba a shekaru 5.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare
NAIJ.com
Mailfire view pixel