Jihar Borno da Adamawa suna jinkairta biyan albashin ma’aikata da yan fansho

Jihar Borno da Adamawa suna jinkairta biyan albashin ma’aikata da yan fansho

- Jihohin arewa maso gabas 2 sun kwashe watanni 6 ba albashi ga ma’aikatansu

- Ma’aikata sun nuna bacin ransu game da rike musu albashi da ake yi

Wata shirin kuntata ma’aikata da gwamnatin jihar Borno ya fara ya sabbaba jinkirta biyan albashin ma’aikata, kudin fansho da gratuti wadanda suka murabus.

Shugaban kungiyar yan kwadago na jihar, Titus Abana, ya bayyana wannan a taron ranan Litinin, 1 ga watan Mayu.

Yace masu jiran fansho wadanda sukayi aiki ga gwamnatin jihar basu iya biyan kudaden hayansu, kudin asibiti, kudin makarantan yara.

Yace duk da cewa an kuntata ma’aikatan, har yanzu basu amu albashinsu bat un watan Yunin 2016.

A jihar Adamawa kuma, Anyi wata yar karamar taraliya taron murnan zagayowar ranan kwadago jiya a Yola, yayinda malaman makarantun gwamnati 2000 suka far ma gwamnan jihar Adamawa, Muhammadu Jibirilla Bindow, akan rashin biyan albashin watanni 5 a jere.

Jihar Borno da Adamawa suna jinkairta biyan albashin ma’aikata da yan fansho

Jihar Borno da Adamawa suna jinkairta biyan albashin ma’aikata da yan fansho

Jami’an tsaro sunyi kokarin hana ma’aikatan wadanda suka daga kwalaye domin zanga-zanga. Shugaban kungiyar kwadago NLC na jihar, Dauda Maina, yayi kira da gwamnan ya biya kudin albashin mutane.

KU KARANTA: Gwamnonin arewa 4 da kujeransu ke rawa

“Malaman makarantun firamare basu jin dadi akan yadda ake cire musu albashi da kuma rashin biyan basussukan suke bi da kuma alawus dinsu. Ba za’ayi iya yaki da rashawa a aikin gwamnati ba idan mutane na cikin halin yunwa da iyalansu.”

Bindow, a wata hira da manema labarai, yace basussukan da ake binsu na gwamnatin baya ne.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel