TOFA: Kwamitin Osinbajo: Allura ta tono garma

TOFA: Kwamitin Osinbajo: Allura ta tono garma

– Ana binciken shugaban Hukumar NIA da aka dakatar

– Shugaba Buhari ya bada umarni a hukunta mara gaskiya

– Sai dai fa yanzu da alamu allura ta kwakulo garma

Kamar yadda aka sani ana ta bincike game da shugaban Hukumar NIA na kasa.

Mataimakin shugaban kasa da kuma wasu mutane 2 aka nada a wannan Kwamiti.

Haka kuma ana binciken Sakataren Gwamnatin Tarayya Mr. Babachir David Lawal.

TOFA: Kwamitin Osinbajo: Allura ta tono garma

Kwamitin Osinbajo na shirin kare aiki

NAIJ.com na samun labari daga Jaridar Daily Trust ta jiya cewa allura fa na daf na tono garma a biciken da Kwamitin mutane 3 da ke kunshe da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Ministan Shari’a Abubakar Malami da mai ba da shawara kan tsaro Babagana Munguno.

KU KARANTA: Zan tona asiri Inji Goodluck Jonathan

TOFA: Kwamitin Osinbajo: Allura ta tono garma

Shugaba Buhari ya nada Kwamiti karkashin Osinbajo

Wata Majiyar sirri ta bayyana cewa an gano cewa kudin da aka samu wanda sun kai Naira Biliyan 15 a wani gida a Ikoyin Jihar Legas ba su cikin kudin da tsohon shugaban kasa ya ware na Hukumar a lokacin yana mulki.

Shugaban NIA din da aka dakatar Ambasada Ayo Oke yayi ikirarin cewa kudin su na cikin abin da tsohon shugaba Jonathan ya ware har Dala Miliyan 289 domin wasu ayyuka na tsaro. Sai dai binciken ya nuna ba haka abin yake ba. Ana dai shirin kammala binciken a kuma kama masu laifi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An saki Jagoran Biyafara daga gidan yari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel