2019: Gwamnonin Jihohi 4 da sai sun yi da gaske

2019: Gwamnonin Jihohi 4 da sai sun yi da gaske

– Wasu Gwamnonin sai sun yi da gaske zuwa shekarar 2019

– Akwai adawar gaske game da kujerun na su

– Musamman irin su Gwamnan Jihar Kano

Wasu Gwamnonin Arewa sai sun dage zuwa shekarar zabe 2019.

Ba don komai ba sai don akwai masu harin kujerun na su.

Gwamnan Kano, Bauchi, Katsina da sauran su na fuskantar wannan barazana.

2019: Gwamnonin Jihohi 4 da sai sun yi da gaske

Gwamnonin Arewa a wani taro

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Sule Lamido na hannun Yan Sanda

1. Gwamnan Bauchi Barista MA Abubakar

Gwamnan na fuskantar barazana daga ‘Yan Majalisun Tarayyar Jihar musamman Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara da kuma har sauran Sanatoci don suna iya kokarin kawo masa cikas.

2. Gwamna Masari na Jihar Katsina

Akwai da dama masu neman kujerar a Jam’iyyar PDP da APC din mai mulki. Ciki dai akwai tsohon Sanatan Arewacin Jihar kuma Minista yanzu watau Hadi Sirika wanda sai Gwamna Aminu Masari yayi da gaske

KU KARANTA: Wani Gwamna yayi wa wata ciki

2019: Gwamnonin Jihohi 4 da sai sun yi da gaske

Ana rikici tsakanin Kwankwaso da Ganduje

3. Gwamna Ganduje na Jihar Kano

Akwai babban rikici tsakanin mabiya Ganduje da kuma na tsohon Gwamna Kwankwasiyya wanda a shekarar 2019 za su gwabza tsakanin su.

4. Gwamna El-Rufai na Kaduna

Akwai baraka a Jam’iyyar APC inda irin su Sanata Shehu Sani da wasu da ke ganin ba ayi da su suka ware gefe guda. Yanzu dai har Sanatan na tsakiya yace zai ja da Gwamnan ba a baki ba kurum zuwa shekarar 2019

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An roki wani Gwamna ka da ya rusa gidaje

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel