Siyasa: Rikici a Jam’iyyar APC mai mulki

Siyasa: Rikici a Jam’iyyar APC mai mulki

– Ana samun rikici a Jam’iyyar APC mai mulki a Katsina

– Jam’iyyar ta rabu kusan barayi har 3

– Jaridar Daily Trust tayi wannan harsashe

Yayin da shekarar 2019 ke shirin matsowa kusa ana fara shirin gyara zaman siyasa.

Dama can mun ce wasu Gwamnonin Arewa sai sun dage zuwa shekarar zaben.

A Jihar Katsina haka tafiyar ta ke tsakanin Gwamna da masu harin kujerar.

Siyasa: Rikici a Jam’iyyar APC mai mulki

Gwamna Masari da shugaba Buhari

NAIJ.com ta bayyana yadda Gwamna Masari na Jihar Katsina ke fuskantar barazana daga masu neman kujerar ta sa. Ciki dai akwai tsohon Sanatan Arewacin Jihar kuma Minista na kusa da shugaba Buhari watau Hadi Sirika.

KU KARANTA: Abin da ya hana ni yin irin na Yaradua-Jonathan

Siyasa: Rikici a Jam’iyyar APC mai mulki

Shugaba Buhari a lokacin zabe

Da alamu Jam’iyyar ta rabu kusan gida 3; tsakanin Mai girma Gwamna Aminu Bello Masari da kuma Sanatan Kudancin Jihar Abu Ibrahim da kuma Ministan sufurin jirgin sama watau Hadi Sirika. Kowane dai ba bako bane a harkar siyasa.

Wasu dai na korafin yadda ake tafiyar da Jam’iyyar inda su ke ganin an watsar da asalin ‘Yan Jam’iyya ba ayi da su. Wannan rikici ne dai ta ci Honarabul Aliyu Sabiu Maduru inda aka tunbuke sa daga kujerar Kakakin Majalisarr dokokin Jihar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An yi kira ayi sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da Yan Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016-
2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016- 2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel