Buhari yayi alkawari ga ma’aikata kan albashinsu

Buhari yayi alkawari ga ma’aikata kan albashinsu

-Buhari yayi jawabi a yau ranan murnan zagayowar ranan kwadago ta duniya

-Gwamnatin tarayya a ranan Litinin tayi alkawari ya ma’aikatan Najeriya akan Karin kudin albashinsu.

Shugaban Muhammadu Buhari ya bayyana wannan ne a sakon sa ga ma’aikata a yau ranan murnan ma’aikatan duniya.

Yace: “ Ina farin cikin sanar da ku cewa gwamnati zata gaggauta rahoton da aka bamu ranan 6 ga watan Afrilun 2017.

“Gwamnatin zata dau matakai wajen tabbatar da aiwatar da rahoton kwamitin da aka nada domin duba al’amarin Karin albashi.

“Za’ayi wannan ne saboda rage halin kuncin da ma’aikata ke fuskanta a Najeriya."

“Ina son in tabbatar muku da cewa gwamnati zata cigaba da yin duk abinda ya kamata wajen bunkasa rayuwan yan Najeriya kuma mafi muhimmanci shine karfafa albashin su.”

Buhari yayi alkawari ga ma’aikata kan albashinsu

Buhari yayi alkawari ga ma’aikata kan albashinsu

Yace yana sane da cewa wannan matsin tattalin arzikinda kasar ta shiga ya tsananta wahalan abubuwa.

Wannan matsin tattalin arziki ya sanya masu kamfanoni sun kulle kamfanoninsu, an sallami ma’aikata da dama, rashin biyan albashi maáikata, da sauran su.

KU KARANTA: PDP tayi alkawarin albashin ma'aikata idan aka zabesu a 2019

Ya yabawa musu da hakurin da sukayi duk da wadannan matsalolin da suke fuskanta.

“Na jinjinawa soyayyarku ga kasa da kuma biyayya ga shugabancin kasan,”

“Saboda haka, ina kira ga yan kwadago su cigaba da mara goyon bayansu ga wannan gwamnati wajen neman zaman lafiya da sulhu.”

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel