An samu sabuwar tawariyya a cikin jam’iyyar PDP

An samu sabuwar tawariyya a cikin jam’iyyar PDP

-Wata sabuwar tsagi ta balle daga cikin jam'iyyar PDP

_Tsagin tayi ma kanta suna PDP gaskiya da gaskiya

-Tawariyyan ta yaba ma tsohon shugaban kasa Jonathan

Wata sabuwar kungiya mai suna ‘PDP gaskiya da gaskiya’ ta bayyana yayin da rikicin cikin gida ya cigaba da dabaibaye jam’iyyar PDP, inji rahoton jaridar Nigerian Tribune.

Kungiyar tawariyyan ta gudanar da taron ta ne a ranar Alhamis din data gabata a garin Abuja inda tace ba zata yarda da farfagandan jam’iyyar APC ba.

KU KARANTA: Sojoji sun hallaka tsagerun matasa 8 a jihar Kros Ribas, dayawa sun samu raunuka

Kungiyar ta fitar da sanarwa wanda ya samu sa hannun shugaban ta Abdullahi Aliyu Babawo da sakataren ta Efiedi Nkonko, inda suka ce “Kungiyar su ta yanke hukuncin wayar da kan yan Najeriya bayan sauraron shawarwari daga mutane daban daban.

An samu sabuwar tawariyya a cikin jam’iyyar PDP

Tawariyya a cikin jam’iyyar PDP

“Zamu cigaba da bayyana ma yan Najeriya tare da tuna musu abubuwan alherin da PDP tayi, tare da wayar musu da kai daga karairayin gwamnatin APC .”

Kungiyar ta yaba ma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sakamakon kokarin dayake yin a ganin ya kawo zaman lafiya a PDP.

Idan ba’a manta ba, NAIJ.com ta ruwaito cewar shugaban PDP Ali Modu Sherif yayi watsi da yunkurin da tsohon shugaba Jonathan keyi na ganin an kawo daidaito a jam’iyyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Najeriya sun koka da shugabannin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel