Murnar ranar ma’aikata: An yi ma Saraki, Dogara da Minista ihun ɓarayi (Bidiyo)

Murnar ranar ma’aikata: An yi ma Saraki, Dogara da Minista ihun ɓarayi (Bidiyo)

-Ma'aikatan Najeriya sun bukaci a biya su karancin albashin N56,000

-Ma'aikatan sun yi ma manyan baki ihun barayi a lokacin da suke jawabi

Yayan kungiyar kwadago ta kasa, NLC sun yi ma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da kuma ministan kwadago ihu tare da kiran su barayi yayin gangamin taron ma’aikatan a yau Litinin 1 ga watan Mayu.

Ma’aikatan sun rikita filin gangamin ne kan bukatarsu na lallai sai gwamnati ta fara biyan su karancin albashi na N56,000, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

KU KARANTA: Matsafa sun aika da wata kurciya mai dauke da asiri jihar Kano

Lamarin yayi kamari ne daidai lokacin da aka kira wakilin ministan kwadago, babban sakatare a ma’aikatan kwadago Abiola Bawa daya fito don yayi jawabi a madadin minista a filin taro na Eagle Square.

Wannan sai ya harzuka ma’aikatan da suke ganin ministan bai mutuntasu ba daya aiko wani ya wakilce shi bayan shi kansa ya kamata ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.

Majiyar NAIJ.com ta bayyana mana daga nan suka fara ihu ‘bama yi, bama yi, bama yi’, ‘Barawo, barawo, barawo!’ ‘A biya mu karancin albashi! A biya mu karancin albashi!’

Hakan yayi matukar bata ma ministan rai, inda ya fasa gabatar da jawabin, ya koma kujerarsa ya zauna. Daga nan sai shuwgabannin NLC suka kira tsohon shugaban kungiyar Adams Oshiomole don ya kwantar da hankalin ma’aikatan, amma ma’aikatan suka cigaba da yi masa ihu.

Murnar ranar ma’aikata: An yi ma Saraki, Dogara da Minista ihun ɓarayi (Bidiyo)

Kwadago

Daga nan sai ma’aikatan suka matsa zuwa inda manyan baki ke zama, hakan ya sanya yansanda korarsu, inda su kuma manyan bakin suka ruga daga wajen.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kun san wanene jagoran zaman lafiya a Najeriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel