Ranan kwadago : Ma’aikata sunyi kukan fitittika, cin mutuncinsu, da cin zarafinsu da kamfanoni ke yi

Ranan kwadago : Ma’aikata sunyi kukan fitittika, cin mutuncinsu, da cin zarafinsu da kamfanoni ke yi

-Ma’aikatan Najeriya sun koka akan yadda ake ci mutuncinsu

-Sun bayyana yadda ake koransu yadda aka ga dama kawai

Wata gungun ma’aikata na kungiyoyin kwadago daban-daban a yau Litinin sun siffanta raba aikin da akeyi, take hakki, kora da rashin kula da ma’aikata da akeyi a fadin kasan nan.

Sun bayyana wannan abu a hira da sukayi da jardar NAN a Legas yayinda suke murnan ranan kwadagon duniya.

Mr Umaru Osbuade na kungiyar masu aikin karafunan Najeriya yace ma’aikatan kamfanonin karafuna na fuskantan cin mutunci inda ake koransu sannan a ake daukansu a matsayin ma’aikatan wucin gadi ko na kwangila.

Rana kwadago : Ma’aikata sunyi kukan koran ma’aikata, cin mutuncinsu, da cin zarafinsu da kamfanoni ke yi

Rana kwadago : Ma’aikata sunyi kukan koran ma’aikata, cin mutuncinsu, da cin zarafinsu da kamfanoni ke yi

Yace: “A matsayimu na ma’aikatan karafuna, ba karamin wulakanci ake mana ba. kafin a tabbatar da ma’aikaci, sai yayi aiki na misalin shekaru 4.

“Abubuwa sun baci sosai a aikin, idan kayi magana, ace ka je ke nemi wani aikin.”

“Kungiyar tana tsoron kira ga yajin aiki saboda bata son wasu ma’aikatannta su rasa ayyukansu.”

KU KARANTA: Abinda wani gwamna yayi da yar bautar kasa

Shugaban kungiyar masu aikin kamfanin Najeriya, Mr Harold Benstowe, ya bayyanawa manema labarai cewa wasu ma’ aikatan akin direba sukewa kamfanonin.

Mr Harold Benstowe, yace ana cin mutuncin ma’aikata yadda ake amfani da su kuma a fitittike sub a tare da gargadi ba.

“Ana daukan ma’aikatan na wucin gadi ne, idan suka gama aikinsu, sai kamfanonin su koresu ba tare da saka musu ba.

“A yanzu haka, muna samun matsala da Dawoo Nig. Ltd., which wacce ta sallami ma’aikata 200 ba tare sakayya ba.”

Ma’aikatan na kira ga gwamnatin tarayya tayi dokar da zai haramta cin mutuncin ma’aikata da kuma take musu hakkinsu.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel