Matsafa sun aika da wata kurciya mai dauke da asiri jihar Kano

Matsafa sun aika da wata kurciya mai dauke da asiri jihar Kano

-Har a wannan zamani mutane na cigaba da yi ma junansu asiri da tsafe tsafe

-An kama wata kurciya a jihar Kano, wanda ake tunanin ta tsafi ce

Allah daya gari bambam, yayin da wasu ke kiwata kurciya domin su siyar ko su ci, wasu kuwa suna kiwata su ne domin ayi amfani da su wajen kulla surkullen ko asiri.

Jaridar Premium Times ta ruwaito labarin wata kurciya da aka kama daure da shirgegen laya a wuyarta a jihar Kano, wanda hakan ke nuni da cewa asiri ne aka shirya ma wani ko wata.

KU KARANTA: Sojoji sun hallaka tsagerun matasa 8 a jihar Kros Ribas, dayawa sun samu raunuka

Ita dai wannan kurciya ta shafe watanni biyar tana gararamba a saririn samaniya tare da saukowa kasa don neman abinci a yankin Daganawa, karamar hukumar Bunkure dake jihar Kano.

Matsafa sun aika da wata kurciya mai dauke da asiri jihar Kano
Kurciya mai laya

To dama dai ita kurciya sau dayawa wadansu kan yi farautar su domin kiwo ko ci ne, hakan ya sanya wasu matasa su biyu Babangida da Shehu sukayi ta fakon kurciyar amma Allah baiyi za su kamata ba sai yanzu.

Matasan su biyu sunce: “Akwai lokacin da alumma suka yi yinkurin harbota da danko wasu da baushe duk muka hana su domin muna zaton hakan.

Cikin ikon Allah a wannan karon muka samo kalli wato tarko muka sashi a cikin gona tare da yafa tsabar gero da dawa nan take ta sauko ta kamaci har ta fada cikin tarkon inda muakayi nasarar kamata.”

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewar bayan yin hakan ne sai matasan suka gano wannan shirgegen laya a wuyan Kurciyar.

Babangida da Shehu basu tsorata da ganin haka ba sai suka cire layar sannan suka warware ta. Sun sanar da cewa an rubuta (Haihata Haihata) da jini a jikin takardan da suka warware da wadansu surkulle ajiki.

Yanzu dai Babangida da Shehu sun ajiye kurciyar suna ta bata abinci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli ra'ayoyin jama'a

Asali: Legit.ng

Online view pixel