Bawan Allah ya sadaukar da N30m da aka bashi kyauta ga iyalan Sojojin da Boko Haram ta kashe

Bawan Allah ya sadaukar da N30m da aka bashi kyauta ga iyalan Sojojin da Boko Haram ta kashe

-Wani dan kasuwa ya jinjina ma sojojin sa kai wato Civilian JTF da suke yaki da Boko Haram

-Alhaji Dalori ya nuna tausayinsa ga iyalan wadanda aka kashe a cikinsu ta hanyar tallafa ma iyalansu

Shugaban wata kamfanin gine gine da sufuri ‘Galaxy Construction and Transportation Services Limited’ Alhaji Babagan Abba Dalori ya sadaukar da naira miliyan 30 da abokanansa suka hada masa a matsayin kyautan aurensa ga iyalan sojojin sa kai, ‘Civlian JTF’ da aka kashe a rikicin Boko Haram.

Alhaji Dalori ya kashe kudin ne wajen siyan kayayyakin abinci da magunguna ga iyalan mamatan, inda ya raba kayayyakin abinci ga iyalai 130, 38 daga cikin yan garin Dalori ne, sauran kuma a hedikwatar Civilian JTF dake garin Maiduguri.

KU KARANTA: Matasa sun afka a gidan wani dan majalisar tarayya su ka yi masa karkaf

Rahoton Daily Trust ya bayyana Alhaji Dalori ya yaba tare da jijina ga sojojin Civilian JTF, inda ya bayyana su a matsayin wasu ginshikai na yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

Bawan Allah ya sadaukar da N30m da aka bashi kyauta ga iyalan Sojojin da Boko Haram ta kashe

Babagana Dalori

“Na bayar da wannan kyauta ne ga iyalan sojojin Civilian JTF da suka rasa rayukansu a yayin kare jama’an mu daga yan ta’ddan Boko Haram, ina fatan wannan zai kara ma sauran kwarin gwiwar cigaba da aikin da suke yi, don kuwa ba zamu bari iyalansu su wulakanta a bayan basu ba.” Inji shi

Bawan Allah ya sadaukar da N30m da aka bashi kyauta ga iyalan Sojojin da Boko Haram ta kashe

Babagana Dalori da Amaryarsa

NAIJ.com ta samu rahoton a ranar Asabar 29 ga watan Afrilu ne aka daura auren Dalori ta matarsa Fatima a garin Maiduguri.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli halin da Boko Haram ta jefa jama'a a Borno

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel