‘Zamu gurfanar da Sule Lamido gaban kotu da zarar mun kammala bincike’ – Yansanda

‘Zamu gurfanar da Sule Lamido gaban kotu da zarar mun kammala bincike’ – Yansanda

-Hukumar yansandan Najeriya taci alwashin gurfanar da Sule Lamido gaban kotu

-Hukumar tace Sule Lamido na furta kalaman da ka ya kawo tashin hankali a al'umma

Mataimakin shugaban yansanda mai kula da sashe na daya, Mista Kayode Aderanti yace zasu gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido gaban kuliya manta sabo da zarar sun kammala bincike.

Aderanti ya bayyana haka ne ta bakin Kaakakin hukumar yansandan sashin DSP Sambo Sokoto yayin dayake ganawa da yan jaridu a ranar Lahadi 30 ga watan Mayu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Matasa sun afka a gidan wani dan majalisar tarayya su ka yi masa karkaf

DSP Sambo yace “Mun gayyaci tsohon gwamnan ne sakamakon korafi da muka samu daga gwamnatin jihar Jigawa a ranar 27 ga watan Afrilu, biyo wasu batutuwa da yayi da ka iya tunzura jama’a ga fadace fadace.”

‘Zamu gurfanar da Sule Lamido gaban kotu da zarar mun kammala bincike’ – Yansanda

Sule Lamido

DPS Sambo yace “Gwamnatin jihar Jigawa ta koka kan wasu kalaman Lamido inda ya shawarci mabiyansa da kasa su yarda a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.”

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Sambo yana cewa ire iren wadannan kalamai sun saba da dokar kasa sashi na 114, don haka zasu gurfanar da Sule Lamido gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike akansa ba tare da bata lokaci ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda kotu ta bada belin wani shugaban inyamurai

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel