Sojoji sun hallaka tsagerun matasa 8 a jihar Kros Ribas, dayawa sun samu raunuka

Sojoji sun hallaka tsagerun matasa 8 a jihar Kros Ribas, dayawa sun samu raunuka

-Rikcin kabilanci na cigaba da ruruwa a kauyukan jihar Kros Ribas

-Al'ummomin garuruwan da suka yi iyaka da jihohin Akwa Ibom dana Kros Ribas ne ke cigaba da baiwa hammata iska

Rahotanni daga jihar Kros Ribas na nuni da cewa dakarun rundunar soji sun kashe akalla wasu tsagerun matasa 8 a garin Ikot Offiong na jihar.

Tsagerun sun gamu da mutuwarsu ne a lokacin da suka ciko kwale kwale da dama inda suka nufi garin Oku Iboku dake karamar hukumar Itu na jihar Akwa Ibom don kai hari ga mutanen garin.

KU KARANTA: An damke Direban ‘Yan Kungiyar Boko Haram

Wannan lamari ya auku ne a ranar Asabar 29 ga watan Afrilu, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya shaida ma NAIJ.com, majiyar ya bayyana cewa matasan sun wurga gurneti cikin garin tare da bude wuta, hakan ya sanya sojojin dake jibge a garin suka mayar da martani, suka kashe mutum takwas.

Sojoji sun hallaka tsagerun matasa 8 a jihar Kros Ribas, dayawa sun samu raunuka

Sojoji

Wani mazaunin garin Itu, Demson Ekong yace “Sojojin sun kawo mana agaji akan lokaci, idan ba haka ba, da tsagerun sun karkashe mu”

Ko a satin daga gabata sai da NAIJ.com ta ruwaito wani kazamin fada daya kaure tsakanin al’ummomin garuruwan biyu, rikicin ya kaure ne sakamakon rikikicin iyakan garuruwan, wannan ne yayi sanadiyyar daukan muggan makamai daga kowane bangare ana yakar juna.

A wancan fadan daya wakana tsakanin al’umman biyu, an samu sama da gawawwaki 20 a wadanda suka mutu a lokacin da matasan garin Oku Iboku sun yi kwantan bauna akan mutanen garin Ikot Offiong.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda shugaba yan Biafra ya samu yanci

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel