Sakacin sanatocin APC yasa Ekweremadu zama mataimakin shugaban majalisa – Inji Saraki

Sakacin sanatocin APC yasa Ekweremadu zama mataimakin shugaban majalisa – Inji Saraki

-Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki yayi bayanin yadda Ekweremadu ya zama mataimakinsa

-Saraki ya jingina laifin ga sanatocin jam'iyyar APC da basu halarci zaman majalisa ba

Shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ya jingina laifi ga sanatocin jam’iyyar APC na yadda suka yi sake sanata Ekweremadu daga jam’iyyar PDP ya zama mataimakin shugaba. Inji rahoton jaridar TheCables.

Saraki ya bayyana haka ne a ranar Litinin 1 ga watan Mayu ta shafinsa na sadarwar zamani Tuwita, yayin da ya musanta batun wani hadin gwiwa tsakaninsa da PDP a lokacin daya zama shugaban majalisar dattawan.

KU KARANTA: An damke Direban ‘Yan Kungiyar Boko Haram An damke Direban ‘Yan Kungiyar Boko Haram

Idan ba’a manta ba an sha rikita rikita a majalisar dattawan a bayan Saraki ya zama shugaban majalisar. A zaman da aka yi ranar da aka zabe shi, Saraki ya samu kuri’u 57, yayin da sauran sanatoci 51 na jam’iyyar APC basa nan, inda suka halarci wani zama da shugaban kasa.

Sakacin sanatocin APC yasa Ekweremadu zama mataimakin shugaban majalisa – Inji Saraki

Saraki da Ekweremadu

NAIJ.com ta ruwaito Saraki yana fadin “Ban shiga wata yarjejeniya da sanatocin PDP ba, saboda ko a lokacin, sanatocin PDP 22 suna tare da ni.

“Kuma ban taba tunanin sanatocin APC ba zasu halarci zaman ba, musamman bayan akawun majalisa ya samu umarni daga shugaban kasa da a rantsar da sanatoci.

“Misali idan wata kungiya bata halarci wasan kwallo ba, sai aka yanke hukuncin an ci ta, shin ya dace taga laifin abokiyar karawarta data halarci wasan.? Don haka sanatocin da suka bari Ekweremadu ya zama mataimakin shugaban majalisa sune wadanda suka tafi suna zaman tattaunawa, a maimakon su shigo majalisa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin majalisar dattawa nada amfani kuwa? Kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel