Naira za ta kara kwari nan ba da dadewa ba

Naira za ta kara kwari nan ba da dadewa ba

– Darajar Naira na shirin mikewa a kasuwa

– An yabawa irin kokarin babban bankin kasar

– CBN na cigaba da sakin daloli domin karya dala

Kwanaki Dala ta dan girgiza kadan a kasuwar canji.

Masana sun ce ana sa rai abubuwa su kara kyau.

Babban bankin kasar na CBN na cigaba da sakin daloli a kasuwa.

Naira za ta kara kwari nan ba da dadewa ba

Babban bankin Najeriya CBN

Mista Muda Lawal shugaban cibiyar ‘yan kasuwa da masu hannun jari na Jihar Legas ya yabawa kokarin babban bankin kasar wajen tsagaita tashin dala a kasuwa. Hukumar dillacin labarai ta bayyana wannan a karshen makon nan.

KU KARANTA: Dala za ta fadi kwanan nan

Naira za ta kara kwari nan ba da dadewa ba

Naira za ta kara daraja kwanan nan

Kamar yadda NAIJ.com ta samu labari dai Lawal ya bayyana cewa bude kofofin saida Dala ga manyan ‘Yan kasuwa zai taimaka wajen daidaita farashin kudin kasashen wajen. Hakan zai taimaka dai wajen samawa masu hannun jari yakini game da tattalin kasar.

Yanzu CBN din na saida Dala ne a kan N360 ga ‘Yan kasuwa masu baza jari wanda su kuma kan saida kan N380 musammam a Birnin Abuja da Garin Legas. Bankin kuma ya ware wasu Dala Miliyan 100 domin masu saye kan sari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yanayin farashin kaya a kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel