Matasa sun afka a gidan wani dan majalisar tarayya su ka yi masa karkaf

Matasa sun afka a gidan wani dan majalisar tarayya su ka yi masa karkaf

- Matasa a garin Gololo da ke cikin Karamar Hukumar Gamawa ta Jihar Bauchi, sun fasa taron raba kayan tallafi da Dan Majalisar Tarayyar su ya shirya.

- Dan Majalisa Honarabul Mohammed Garba Gololo ya shirya taron raba kayan ne a kauyen haihuwar sa, Gololo a ranar Lahadin da ta gabata.

- Baya ga fasa taron, matasan sun kutsa kai cikin sabon gidan Dan Majalisar suka yi wa kayan gidan karkaf.

NAIJ.com ta samu labarin an sace talabijin, bidiyo, rikoda, firji, da duk wani abin amfanin da ke cikin gidan, hatta tagogin gidan sai da aka balle.

Ganau ba jiyau ba ta tabbatar wa majiyar mu cewa hatta motar da Mohammed Garba Ke ciki sai da aka fasa gilashin ta yayin da ya yi niyyar ficewa daga wurin taron, inda matasa ‘yan baberiya su ka nemi yi masa kofar-raggo su na cewa “Ba ma yi! Ba ma yi”, a lokaci guda kuma su na jifa.

Matasa sun afka a gidan wani dan majalisar tarayya su ka yi masa karkaf

Matasa sun afka a gidan wani dan majalisar tarayya su ka yi masa karkaf

KU KARANTA: Jonathan zai iya shiga cikin matsala

Duk wani kokarin jin ta bakin sa ya ci tura, domin wayar sa a kashe ta ke. Sai dai daya daga cikin iyalan sa ya tabbatar da cewa tabbas an fasa gidan an yi sata, amma aikin barayi ne, ba daga rudanin siyasa ba ne.

Wani dan garin mai suna Salisu, ya ce lokacin da abin ya faru ya na cikin garin Gololo, amma ba a daki Honarabul ba, sai dai an fasa gilashin motar sa. Kuma a cewar sa, sharrin ‘yan adawa ne kawai.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel