An damke Direban ‘Yan Kungiyar Boko Haram

An damke Direban ‘Yan Kungiyar Boko Haram

– An yi nasarar damke wani Direban ‘Yan Kungiyar Boko Haram

– Wannan mutumi shi yake kawowa ‘Yan ta’addan abinci da man fetur

– Ana cigaba da murkushe ragowar ‘Yan Boko Haram

Jami’an ‘Yan Sanda sun yi nasarar damke wanda ke kai wa ‘Yan Boko Haram kaya.

Modu Mustafa shi ke ba ‘Yan ta’addan abinci da man fetur.

Hukumar ‘Yan Sanda ta kasa ce dai da wannan kokari.

An damke Direban ‘Yan Kungiyar Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya

NAIJ.com na da labarin cewa Jami’an ‘Yan Sanda sun yi nasarar damke wanda ke kai wa ‘Yan Boko Haram kayan abinci da kuma man fetur a Jiya Lahadi. Wannan mutumi mai suna Modu Mustafa ne ke kai sayawa ‘Yan ta’addan kaya.

KU KARANTA: Yan Sanda sun tsare wani tsohon Gwamna

An damke Direban ‘Yan Kungiyar Boko Haram

'Yan kato d a gora na yakar ‘Yan Kungiyar Boko Haram

Damian Chukwu watau Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Borno ya bayyanawa manema labarai wannan a Maiduguri. An yi nasarar cafke sa ne bayan an samu labari daga bakin Jama’a. Bayan an damke sa dai ya tabbatar da cewa wannan aikin sa ne. Za a mika shi zuwa Sojojin kasar.

Yanzu haka dai Mutanen Garin Madagali su na ta bikin dawowa gidajen su bayan an ga bayan ‘Yan Kungiyar ta’addan na Boko Haram. Sai dai fa an yi raga-raga da Garin ana sa rai Gwamnati ta kawo wani doki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za a raba kasar nan ne?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel