Zan fallasa yadda akayi Buhari ya kada ni a zaben 2015 - Jonathan

Zan fallasa yadda akayi Buhari ya kada ni a zaben 2015 - Jonathan

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya sha alwashin bayyana hakikanin gaskiyar abubuwan da suka auku a zaben 2015.

Jonathan ya yi wannan ikirari ne bayan fitowar wani littafi mai dauke da ba'asin 'yan siyasa kan zaben 2015, wanda Jonathan ya sha kaye. Jonathan ya hakikance kan cewar littafin yana cike da kura-kure da kuma kage.

NAIJ.com ta na nuni da idan mai karatu bai manta ba a cikin littafin Jonathan ya bayyana cewar tsohon Shugaban PDP Ahmed Mu'azu da wasu dattawan Arewa su suka ci amanarsa har ta kai ga ya fadi zabe.

Abun jira a gani dai anan shine, Jonathan zai fallasa mutanen da suka karbi kudi a hunnun shi da sunan za su kawo kuri'un Arewa ne, ko kuma zai fallasa yadda aka yi masa magudin zabe ne?

Zan fallasa yadda akayi Buhari ya kada ni a zaben 2015 - Jonathan

Zan fallasa yadda akayi Buhari ya kada ni a zaben 2015 - Jonathan

KU KARANTA: Sai da na gargadi Jonathan kan makircin yan arewa - David Mark

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa tuni ya yafewa mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na ll bisa shisshigin da yake yi masa, amma gwamnatin jihar za ta cigaba da binciken zargin almubazzaranci da ake yi wa masarautar Kano.

Gwamnan ya bayyana haka ne bayan wani zama na musamman da majalisar hadin gwiwa ta gwamnoni da sarakunan Arewa suka kira a Kaduna, domin sasanta takaddamar da ta taso tsakanin gwamnatin jihar Kano da masarautar, wanda har wasu ke kira da a sauke sarkin daga karagarsa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare
NAIJ.com
Mailfire view pixel