Zamu cigaba da bincikar Sarki Sanusi bisa almubazaranci - Ganduje

Zamu cigaba da bincikar Sarki Sanusi bisa almubazaranci - Ganduje

- Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa tuni ya yafewa mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na ll bisa shisshigin da yake yi masa

- Amma gwamnatin jihar za ta cigaba da binciken zargin almubazzaranci da ake yi wa masarautar Kano.

Gwamnan ya bayyana haka ne bayan wani zama na musamman da majalisar hadin gwiwa ta gwamnoni da sarakunan Arewa suka kira a Kaduna, domin sasanta takaddamar da ta taso tsakanin gwamnatin jihar Kano da masarautar, wanda har wasu ke kira da a sauke sarkin daga karagarsa.

NAIJ.com sun ruwaito cewa rahotanni sun bayyana cewa, a yayin zaman sasantawar Sarkin Kano Sanusi na ll ya nemi gafarar Gwamna Ganduje, tare da bayyana cewa har yanzu yana koyon zama a sabon yanayin da ya samu kansa a ciki ne, kasancewar sa mai nazarin harkokin tattalin arziki da zamantakewa, ba domin wulakanci da son nuna isa ba.

Zamu cigaba da bincikar Sarki Sanusi bisa almubazaranci - Ganduje

Zamu cigaba da bincikar Sarki Sanusi bisa almubazaranci - Ganduje

KU KARANTA: Dalilin da yasa muka kama Sule Lamido - Yan sanda

Don haka ya ce, zai yi kokarin ganin ya koyi rayuwar sarauta karkashin jagorancin Gwamna mai cikakken iko, ta yadda zai rika yi wa bakin sa linzami da yin kawaici.

Wasu da suka yi nazarin yadda taron ya gudana sun bayyana cewa, takaddamar da ta faru tsakanin bangarorin biyu siyasa ce kawai, domin an jiyo wasu daga cikin mukarraban Gwamnan na bayyana cewa, idan aka zubawa Sarkin ido zai yi musu sakiyar da ba ruwa, idan zabe ya gabato. Don haka suke ganin dacewar a taka masa burki, tun kafin ya barar musu da garin da suke sha.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel