‘Yan Sanda za su cigaba da tsare wani tsohon Gwamna

‘Yan Sanda za su cigaba da tsare wani tsohon Gwamna

–Yan Sanda sun kama tsohon Gwamnan Jigawa

– Ana zargin Lamido da kokarin tada fitina a Jihar Jigawa

– Ba za a saki tsohon Gwamnan ba zai an gama bincike

Hukumar ‘Yan Sanda ta damke wani tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido.

AIG na Yankin ya bayyana cewa ba za a saki tsohon Gwamnan ba tukun.

Ana nan tsare da Lamido har sai an kammala bincike.

‘Yan Sanda za su cigaba da tsare wani tsohon Gwamna

Tsohon Gwamna Sule Lamido

NAIJ.com ta kawo labarin cewa Jami’an ‘Yan Sanda sun yi nasarar damke wanda ke kai wa ‘Yan Boko Haram kayan abinci da kuma man fetur a Jiya Lahadi. Wannan mutumi mai suna Modu Mustafa ne ke kai sayawa ‘Yan ta’addan kaya.

KU KARANTA: Abin da ya sa aka kama Lamido

‘Yan Sanda za su cigaba da tsare wani tsohon Gwamna

An kama tsohon Gwamna Lamido

Haka kuma ‘Yan Sanda su na rike da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido. Gwamnan ya mika kan sa ne a gaban ‘Yan Sandan tun kafin a fito neman sa. Mataimakin Sufeta na Yankin Kano ya bayyana cewa za a cigaba da tsare sa sai an kammala bincike.

An tsare tsohon Gwamnan ne saboda wasu kalamai da yayi kwanaki a gidan Rediyo inda yake kokari kawo rikici a zaben kananan Hukumomin Jihar. Wannan din dai babban laifi ne a tsarin dokar kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jagoran Biyafara ya bar Gidan Yari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel