Ra'ayi : Rashin lafiyar Buhari; Kuskure ne mu jira a sake yi mana irin ta Yar'adua

Ra'ayi : Rashin lafiyar Buhari; Kuskure ne mu jira a sake yi mana irin ta Yar'adua

Wannan rubutu ra'ayin marburucin ne ba ra'ayin jaridar NAIJ.com Hausa ba.

Ra'ayin Sheriff Almuhajir.

Ni fa ina gani ya kamata 'yan Arewa su ajiye zancen soyayya ko kiyayya a kan maganar Buhari, haka nan makusantan Buhari su dai na mana karya akan lafiyarshi. Haka aka yi ta boye-boye lokacin Yar'adua, daga baya muka dawo muna kuka tare.

Tabbas rashin lafiya ce za ta hana Buhari zaman majalisar zartarwa har sau uku, ita ce za ta hana shi fita ofishinsa gaba daya, kuma ita ce za ta hana shi fitowa sallarJjuma'a. Amma saboda yanke uzuri za mu saurara zuwa Juma'ah biyu nan gaba, daga nan ba ma bukatar bayaninsu.

Idan har Allah Ya jarrabci Buhari da ciwon da zai hana shi aiki ne (Allah kiyaye) to kuskure ne mu jira a sake mana irin ta Yar'adua, ya kamata mu fara tsare-tsare tun kafin su Tinubu da Pastor Adeboye su nada mana mataimaki. Na wan ba ku mance ba yadda wasu su ka zauna su ka dauko Namadi Sambo da bai tabuka komai ba har aka gama gwamnati.

KU KARANTA: Buhari bai iya ci ko sha - Sahara reporters

Wannan dai ba karamin tashin hankali ba ne, amma dai sani da sauri zai fi mana. Irin Wannan shawarar ce Babagana Kingibe ya bai wa Yar'adua, aka tumbuke shi, daga baya duk mu ka dandana kudarmu.

Allah ka bai wa shugaban kasarmu lafiya mai dorewa da za ta raka shi ko da zuwa karshen zabe mai zuwa ne.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel