Majalisar wakilai na shirye da tabbatar da dokar karin albashin ma’aikata – Kakaki Yakubu Dogara

Majalisar wakilai na shirye da tabbatar da dokar karin albashin ma’aikata – Kakaki Yakubu Dogara

-Yakubu Dogara yayi maganan da zai kwantarwa ma’aikata hankali

-Ya yabawa ma’aikatan Najeriya wajen kokarinsu wajen kawo cigaban kasa

Kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara, yace majalisa na shirye da tabbatar da dokan Karin albashin ma’aikatan Najeriya.

Dogara ya bayyana hakan ne a wata jawabin da mai magana da yawunsa, Turaki Hassan a rattaba hannun a ranan Lahadi, 30 ga watan Afrilu domin na sakon murnarsa ga ranan yan ma’ aikatan kwadagon Najeriya

“Ina taya dukkan ma’aiktan Najeriya murnan yayinda suka hada kai da sauran ma’aikatan duniya wajen murnan zagayowar ranan ma’aikatan duniya.

“Ina son tabbatar muku da cewa majalisan dokoki musamman majalisan wakilai ta 8 ta zange dantse wajen tabbatar d cewa ta gabatar da sauran dokokin wanda zai taimaka wajen bunkasa rayuwan ma’aikata da kuma kara kudin albashin su."

Majalisar wakilai na shirye da tabbatar da dokar karin albashin ma’aikata – Kakaki Yakubu Dogara

Majalisar wakilai na shirye da tabbatar da dokar karin albashin ma’aikata – Kakaki Yakubu Dogara

Dogara yayi kira ga ma’aikata to bada karfin guiwarsu wajen taimakawa shirye-shiryen gwamnati da ayyuka.

KU KARANTA: Akwai rikici tsakanin fadar shugaban kasa da majalisa

Yace: “ Yayinda kuke murnan wannan rana mai tarihi, ina son tuna ma yan Najeriya kokarin da ma’aikata key i wajen kawo cigaban kasa da kuma taimakawa shirye-shiryen gwamnati domin bunkasa rayuwar yan Najeriya."

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel