Za a bude kamfanin da zai samawa matasa fiye da 5,000 aikin yi a jihar Jigawa

Za a bude kamfanin da zai samawa matasa fiye da 5,000 aikin yi a jihar Jigawa

- Wani shahararran dan kasuwa na kasar China zai bude wata sabuwar kamfanin a jihar Jigawa

- Kamfanin bayan aka kammala ta zai samawa matasan jihar Jigawa fiye da 5,000 aiyukan yi

- Gwamnan jihar jigawa ya ce rukunin masana'antun zai kasance mafi girma idan an kamala

Shahararran dan kasuwan nan na kasar China, wato Mista Lee, zai bude kamfanin da zai samawa matasan jihar Jigawa fiye da 5,000 aiyukan yi.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar a ranar Lahadi, 30 ga watamn Afrilu ya aza harsashin gina kamfanin sukari na kamfanin Great Northen Agri Business a garin Chiroma dake karamar hukumar Gagarawa.

A yayin da yake jawabi a wajen bikin aza harsashin gina kamfanin, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya ce aikin ba wai kawai na samar da kamfanin sukari bane, amma wani rukuni ne na masana'antu da zai samar da sukari, sinadarin dandanon girki, kamfanin samar da takin zamani da kuma karamar tashar samar da wutan Lantarki mai karfin megawatts 17.

Za a bude kamfanin da zai samawa matasa fiye da 5,000 aikin yi a jihar Jigawa

Shugaban rukunin kamfanonin na Lee, Mista Sheau Fung Lee ya na jawabi a wajen taron

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, wannan rukunin masana'antun, shine zai kasance mafi girma idan an kammala, wanda idan aka kammala za ake samar da fiye da tan 100,000 na sukari a duk shekara.

Za a bude kamfanin da zai samawa matasa fiye da 5,000 aikin yi a jihar Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar da Mista Sheau Fung Lee a wajen taron

KU KARANTA KUMA: Ba mamaki darajar Dala ta fadi kasa

Kamar yadda NAIJ.com ke da labara, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya kara da cewa an baiwa kamfanin kadada na kasa mai murabba'in kadada 12,000 wanda kamfanin ta biya masu filayen hakkokin su (diyya), inda aka ware kadada 6,000 domin kasancewa bangaren da kamfanin sukarin zasu nome raken da zasu yi amfani da shi na samar da sukarin, a yayinda saura kadada 6,000 za a yayyanka su domin kara maidawa ga manoman da aka karbi gonakin su a shirin su na tallafawa manoman ta hanyar saye abinda suka nome.

Gwamnan ya kuma yabawa Mai Martaba sarkin Gumel Alhaji Ahmad Muhammad Sani III akan irin shawarwarin dattako da yake baiwa al'umar yankin da kuma masu ruwa da tsaki a samar da masana'antar a jihar Jigawa.

Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga shugaban rukunin masana'antun Lee bisa ga jajircewar sa wajen samar da masana'antar duk da karayar tattalin arziki da aka samu da kuma irin kalubalen da ya fuskanta daga wasa marasa kishin al'umar su.

A nasa jawabin, Shugaban rukunin Kamfanonin na Lee, Mista Sheau Fung Lee ya bayyana cewa a harabar kamfanin za a samar da ɗakin shan magani, tashar kashe gobara da sauran wasu ababen amfanarwa ga al'umar yankin.

Shi ma a jawabinsa, ministan noma Mista Audu Ogbeh ya ce kasar Najeriya zata cigaba da kulla huldar cinikayya da zuba jari tsakanin ta da Kasar China.

KU KARANTA KUMA: Manoma a Arewa suna ci gaba da keta hazo suna sauke farali

Shima a nasa jawabin, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Mista Godwin Emefiele ya yabawa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na samar da kyakkyawar yanayi ga masu zuba jari da suke nuna sha'awar su wajen zuba jari a Jihar.

Shi kuwa Mai Martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmad Muhammad Sani yabawa Mista Lee yayi akan kokarin sa na kafa masana'antar, inda ya kara da cewa samar da kamfanin zai samar da ayyukan yi ga ɗumbin al'umar yankin.

Mai Martaba Sarkin ya kuma tabbatar da cewa da shi da masarautar sa, zasu cigaba da bada gudunmawa da goyon bayan su a kowane mataki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel