Dalilin da ya sa muka kama Sule Lamido - Inji Rundunar ‘yan sanda

Dalilin da ya sa muka kama Sule Lamido - Inji Rundunar ‘yan sanda

- Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama Sule Lamido bisa kalaman tunzura al'umma

- DSP ya ce babban laifi ne wani ya furta kalaman da za su iya tayar da hankali ko kuma hatsaniya

- Sambo ya tabattar da cewa bai san lokacin da za a sake tsohon gwamnan ba

Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta ce ta kama tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido bisa kalaman tunzura al'umma.

DSP, Sambo Sakkwato wanda shi ne mai magana da yawun rundunar 'yan sandan shiyya ta daya da ke Kano, ya shaida cewa sun samu korafi ne daga gwamnatin jihar Jigawa kan kalaman tunzura jama'a.

NAIJ.com ta ruwaito cewa DSP ya ce babban laifi ne wani ya furta kalaman da za su iya tayar da hankali ko kuma hatsaniya.

DSP Sambo ya ce duk da cewa rundunar ta gayyaci tsohon gwamnan ne amma ba zata iya tabbatar da hakikanin lokacin da za a sake shi ba.

An dai kama Sule Lamido ne a gidansa da ke sharada a Kano da safiyar ranar Lahadi, 30 ga watan Afrilu.

Sule Lamido dai ya bukaci magoya bayansa na jam'iyyar PDP a jihar Jigawa da su kare kuri'unsu a zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.

KU KARANTA KUMA: Yadda shugabancin ya musanta rahoto cewa Buhari na rashin lafiya sosai da kuma ba zai iya ci ko sha

Wani makusancin Sule Lamidon, Alhaji Ndagi Malanmadori ya shaida cewa: " Sule Lamido ya nanata abin da shugaba Buhari yake fada ne cewa 'A kasa, a tsare sannan a raka' saboda haka ni ban ga laifin mai gida ba."

Alhaji Sule Lamido, yana daya daga cikin jigajigan 'ya'yan babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, kuma a 'yan kwanakin nan, ya yi ta sukar irin kamun ludayin gwamnatin kasar ta jam'iyyar APC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali inda wani matashi ya ce ya kamata a yi wa shugabanin Najeriya jana'izar gama gari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel